Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com/
Page 9️⃣ & 1️⃣0️⃣
Barci mai nauyi Jiddo take yi, amma a cikin barcin ma tana ta faman sambatu tana kiran sunan Innawuro da Babawuro. Nurses din dake kanta sai tausayinta suke ji, ganin yadda take zabura lokaci bayan lokaci. Nazeefa kuwa tana zaune a gefen gadon, idanunta sun yi jawur saboda kukan da take yi. Ta kasa daina tunanin yadda rayuwar wannan yarinya ta kasance a cikin daji ita kadai.
A can gidan Tahreem kuwa, fada sosai take yi wa sauran matan gidan. “Daga yau, duk wacce ba za ta yi sallah akan lokaci ba, to ta tattara kayanta ta bar min gida! Ba zan zama silar fushin Allah akan kowa ba,” Tahreem ta fada tana huci. Talatu da sauran matan suka shiga daki jikinsu na rawa, kowace tana neman darduma don yin sallah.
Tahreem ta koma dakin Nazeefa ta zauna, tana tunanin maganar yarinyar nan bafullatana. Duk da tana nuna halin ko-in-kula, amma a ranta tana jin wani irin tausayi yana ratsata. Ta dauki wayarta ta kira Malam Dauda. “Malam Dauda, ya jikin yarinyar? Akwai wani cigaba?”
Malam Dauda ya amsa mata da cewa, “Hajiya tana barci har yanzu, amma likita yace tana bukatar kulawa ta musamman saboda firgicin da ta shiga.” Tahreem ta ja numfashi, sannan tace, “To shikenan, duk abinda ake bukata a asibitin ka sanar dani.”
Bayan awa biyu, Jiddo ta fara bude idonta a hankali. Hasken dakin asibitin ya fara dukan idonta, ta fara rarraba ido tana neman inda take. Ganin Nazeefa a kanta ya sa ta fara kokarin tashi da sauri. “Ina yarinyar nan? Ina birran nan?” ta fada cikin muryar kuka.
Nazeefa ta kamo hannunta, “Kwanta Jiddo, ba kowa a nan sai alheri. Kina asibiti ne, kin tsira daga dajin nan.” Jiddo ta kalli jikinta taga an canja mata kaya, ta kalli hannunta taga ruwan asibiti (drip) yana ratsa jikinta. Ta fara kuka a hankali, “Ina Innawuro na? Sun kashe kowa, ni kadai suka bari…”
Ku cigaba da bibiyanmu a arewamusix.com domin jin yadda zata kaya tsakanin Jiddo da su Tahreem.