Yadda Zaka Dawo Da Layin Da Aka Rufe Maka Na MTN
Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokacinda fatan kuna cikin koshin lafiya.
Shin kana da cikin wanda mtn suna rufe masa layi? Kamar yadda kuka sani kamfanin mtn suna toshe layikan mutane musamman wadanda basu hada layin su da nin number tasu ta ainihiba, mafi akasarin sim din da suke rufewa shine wanda nin ya sauka kuma baka gyaraba kokuma wanda yayi link na sim dinsa da nin wacce ba tasaba, hakanne yasa suke rufe layuka ta yadda dole sai kaje kamfanin layin ko wani branch nasu domin a gyara maka.
Ganin yadda mutane suke tururywar zuwa kamfanin layi mafi kusa dasu, hakan yasa kamfanin ya fitar da link wanda ya bawa kowa damar gyara matsalar sim dinsa da kansa.
Idan kana daga cikin wanda sim dinsa ya samu matsala ga yadda zaka gyara.
Abubuwan da ake bukata:
- Phone number
- Email address
- Nin mumber
Da farko zaka shiga wannan link din dake kasa
👇
https://ninlinking.mtn.ng/
Bayan link din ya bude zakaga wajen da zaka sanya number waya(wacce aka rufe din) da kuma email dinka
Bayan ka sanya number waya da email saika danna check nin status nan take zasu tura maka da otp a Email dinka.
Daga nan saika shiga email dinka kayi copy na otp din kazo kasa a wajen da sukace asaka.
Bayan ka saka sai kayi next daga nan zasu kawoka wajen da zaka sanya Nin number ka saika sanya.
Bayan kasa daga nan shikkenan inde Sim din kaine kayi masa register duka bayanan dake sim din nakane to shikkenan zasuyi review su gyarama layinka.
Amma idan ba kaine kayi masa register ba to gaskiya shikkenan saide kayi hakuri sabo da dole sai wanda yayi register sim din sannan zai iya gyaransa.
Allah ya bamu sa’a