Yadda Zaka Bude Bitmart Exchanger Domin sayar Da AvaCoin Dinka
Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana lafiya.
Kamar yadda kuka sani a yau 30/7/2024 za ayi listing na avacoin a wasu daga cikin exchanger da muke dasu za ayi listining dinne a Bitget exchanger da kuma Bitmart exchanger za ayi listining din daga karfe 11:00am
Dan haka wannaj darasin namu zai nuna muku yadda zaku bude exchanger na bitmart kasancewar bitget tana bada matsala wajen budewa, dan haka ku tsaya ku nutsu domin ku bude kuyi verify cikin sauki domin sayar da avacoin dinku.
Da farko zaku danna Link dinnan domin saukar da bitmart din 👇
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.bitmart.bitmarket
Bayan kun saukar da ita saiku bude sannan ku shiga Get started
Daga nan zai kawoku shafin da zakuyi create account saiku shigar da email dinku sannan ku kirkiri password mai karfi ku shigar dashi
Daga nan zata kawoku wajen da zakuyi verify sai ku duba email dinku zasu tura muku code sai kuje email din kuyi copy kuzo kusa
Bayan kun gama login in daga nan zata kaiku cikin exchanger yanzu abun da zakuyi shine verify, saiku duba wajen icon na profile dinku saiku danna
Daga nan saiku danna karaminarrow dake gaban email dinku
Daga nan zai kawoku wajen da zakuga verify saiku danna
Daga nan zai kawoku kuyi verify sai kuyi verify, shi verify din kala biyu ne akwai Lavel 1 akwai lavel 2, idan da dama kowanne kuyi domin babu wahala.
Bayan kun kammala verifying shikkenan yanzu Bitmart exchanger ku ta zama Ready dan haka da zarar lokaci yayi kun turo avacoin dinku ciki nan take zaku iya sayar dashi ku karbi kudinku.
Allah ya bada sa’a