Yadda Ake Cirema Photo Background A Wayar Android Kasa Wanda Kakeso:

Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da warhaka, a yau zamuyi bayanine dangane da canjin background na hoto, yawancin mutane suna daukan hoto a waya kuma sunason su cire background na wannan hoto wato su canja shi zuwa wani daban, amma wasu basu san cewar zasu iyayi da wayoyin hannunsu ba, saidai da computer toh yanzu ga hanya mafi sauki da zakuyi wannan abun ba tareda kun samu wata matsalaba.
Toh dafarko dai zamu fara da cire background na hoto wanda daga nan zaku daura wanda kuke so.
Dafarko saiku shiga nan https://www.remove.bg/ kuna shiga zakuga inda aka rubuta upload saiku taba kansa zaikaiku inda zaku dauko hoton dake cikin wayanku saiku duba inda hoton yake ku dauko saiku taba kan hoton, kuna tabawa toh daganan zakuga inda aka rubuta AUTO ya cire ma wannan background din cikin sauki saiku danna kan download saiku dakko hoton dakuka cirewa background din akan wayanku shikenan kun gama da cire background na hoto.
Abun da yasa mukayi aiki da wannan shine yafi sauki duk aciki, wanda ba saika sha wahala ba koh kuma ka iya computer kawai mb kake bukata ba ruwanka da computer
Sai kuma yadda zaka daura hoto akan wani background daban banda wanda ka cire kasa wanda kake so
Dafarko dai akwai app daban da wanda ake aiki dasu domin cire koh saka background koh kuma ince hoto editing koh graphic design kuma duk a wayan android din.
Zaka shiga play store kayi downloading na PIXEL LAB application inkayi downloading dinsa saika bude ka shiga zakaga cikin ya bude.
Kana shiga saika taba inda aka rubuta wannan plus din saika danna zai kaika kan gellary na cikin wayanka saika dakko hoton daka cirewa background saika taba kansa kana taba kansa zaikaika inda zaka dai-daita hoton kayi cropping nasa saika dannan OK
Sai kuma idan kanaso ka canja colour ne kawai na abun ma’ana kanaso bayansa ya zama ja ko kore koh blue saika taba inda aka rubuta arrow dinnan idan ka taba zakaga inda aka rubuta colour a jerin abubuwan da zasu fitto saika taba kan kalan da kakeso saikasa a wurin shikenan kaga anan zaka iya yin passport a wayanka kawai printing zakaje kayi shikenan ka gama.
Sai kuma wanda kakeso kasa a wani background din daban kaman kadau hoto kana so ka canja bayan gaba daya toh shi idan ka dakko hoton a gallery din wayanka saika taba inda yayi kaman circle dinnan kana tabawa a cikin abubuwan da zasu fito saika duba inda aka rubuta import saika taba daga nan zai kaika cikin gallery din wayanka saika dakko hoton da kakeso kasa a bayan naka saika taba kansa kana tabawa zakaga yazo kan screen na wayanka saika danyi gefe kadan zakaga inda aka rubuta TO BACK saika taba daga nan zakaga hoton naka ya koma baya shikenan ya zauna a background dinka saikasaita su dai-dai yadda kakeso kayi saved dinshi a hoto zuwa gallery din wayanka, shikenan ka gama.