Yadda Zaka Gane Boyayyan Lamba Wato (Private Number) Idan An Kiraka Ba Tare Da Wani Application Ba:

Assalamu alaikum warahmatullah, barkanmu da warhaka, ayau zamuyi muku bayanine dangane da hanya mafi sauki da zaka gano private number shine ta hanyar dabarar “Call Recording”

Toh dafarko dai idan kanason fitar da numbern da aka kiraka dashi ko da yana private ne toh zakayi recording din call din ko da na secon 1 ne.

Idan wayar ka tana auto record ne shikenan in kuma ba tana Auto record bane toh da zarar ka daga kiran saika danna record kasamu koh da 1 second ne, bayan kagama call din sai kaje wajen “File Manager” na wayarka kaduba foldern da ke storing call record din misali “Phone Memory > Music > PhoneRecord”.

Ya danganta da wayar da kake amfani dashi sai kayi sorting din file din based on time, amma sorting din ba dole bane nasakashi ne saboda in dai kayi sort by date ko by time na karshe shine zaizo farko.

Wasu wayoyin suna ajiye koh wane irin Recording a folder daban-daban wasu kuma direct a cikin PhoneRecord dinka zaka sameshi.

Idan Foldern daban-dabanne toh saika duba sunan foldern shine Phone Numbern, ma’ana zakaga yayi saving din sunan Foldern da Phone Numbern misali 08026.

Wani lokacin zakaga yahada Date din wannan ranar da Phone Number amma zai saka underscore _.
Misali 20230711_07068*.

Haka inma duka files din acikin folder “PhoneRecord” ya ajiye zakaga shima sunan Recording din da Phone Number ko hade da date din, amma dai mafi yawanci a folder daban-daban yake ajiye kowanne Phone Call Recording da Phone Numbern a matsayin sunan Foldern.

Karin bayani: a wayar Android akeyi ba yayi a waya keyboard.

Apply Now

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button