Muhimmiyar Sanarwa Game Da Daukan Ma’aikata A Hukumomin Tsaro Na Nigeria

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ta amince da fara daukar sabbin ma’aikata a wasu daga cikin manyan hukumomin tsaro na ƙasa. Wannan daukar aiki zai shafi hukumomi guda huɗu da ke ƙarƙashin hukumar Civil Defence, Correctional, Fire and Immigration Services Board (CDCFIB). Hukumomin da abin ya shafa sun haɗa da: Hukumar Gyaran Hali (Correctional Service), Hukumar Shige da Fice ta Ƙasa (Nigeria Immigration Service), Hukumar Kare Rayuka da Dukiyoyin Fararen Hula (NSCDC), da kuma Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa (Federal Fire Service).

Ana sa ran za a bude shafin yanar gizo na musamman domin yin rijistar masu neman aikin nan ba da jimawa ba. Saboda haka, yana da kyau masu sha’awar shiga cikin wannan tsarin su fara shiri tun da wuri. Wannan ya haɗa da tanadi na takardun da ake buƙata da kuma shirye-shiryen jarabawar tantancewa da ake sa ran za a gudanar.

Daukar ma’aikatan zai ba da dama ga matasa da dama su samu aikin yi a cikin sahun hukumomin tsaro, tare da taimaka wa gwamnati wajen ƙarfafa ayyukan tsaro da kare lafiyar jama’a da dukiyoyinsu a fadin ƙasar. Wannan mataki na gwamnatin Tarayya na daya daga cikin hanyoyin rage rashin aikin yi da kuma cike guraben da ke akwai a wadannan hukumomi.

Daga ƙarshe, ana ƙarfafa matasa da sauran ’yan Najeriya masu sha’awar aiki a wadannan hukumomi su kasance cikin shiri, su sa ido kan sanarwar bude dandalin rijista, tare da bin dukkan ka’idoji da sharuɗɗan da za a gindaya wajen cika fam da halartar tantancewa.

Ga adadin ma’aikatan da za a dauka a kowace hukuma a cikin wannan sabon shirin daukar aiki da Gwamnatin Tarayya ta amince da shi:

Hukumar Gyaran Hali (Nigeria Correctional Service) – mutum 5,150

Hukumar Shige da Fice (Nigeria Immigration Service) – mutum 10,000

Hukumar Kashe Gobara ta Ƙasa (Federal Fire Service) – mutum 5,000

Hukumar Kare Fararen Hula (Nigeria Security and Civil Defence Corps – NSCDC) – mutum 10,000

Hukumar CDCFIB kanta – mutum 209

Za a bude wani dandalin yin rajista na musamman (online portal) domin bai wa duk wani dan Najeriya mai cancanta damar cike fom din neman aikin. Ana sa ran wannan rajistar za ta kasance a bude na tsawon makonni uku kacal (3 weeks). Saboda haka, ana shawartar masu niyyar nema su kasance cikin shiri, su tanadi dukkan bayanan da ake bukata, domin kada su bari lokaci ya kure musu.

Wannan dama ce babba ga matasa da ke neman aikin yi a hukumomin gwamnati, musamman a bangaren tsaro da hidimar kasa.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button