Auren Huce Haushi

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com

AUREN HUCE HAUSHI

Da sunan Allah Mai Rahama Mai jinkai salati da daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban mu Annabi Muhammad Swallallahu Alaihi Wasallam

Related Articles

Page 60.

_____Suna biye da doctors din har suka shiga dakin abinda suka gani ya daga musu hankali, jikin Baba malam ne yake wata irin jijjiga Kamar Wanda yake ciwon tsintsinko irin na Mata masu haihuwa Abba dasu Abubakar suna ta faman tofa Masa addu’a, ganin lotoci sun shigo yasa su Abba suka matsa suka Basu guri, tamabaya likitan ya jefo musu.
“Ko akwai abinda ya faru Wanda ya haddasa Masa hakan ko Kuma an fada Masa abinda ya tada Masa hankali ne?”.
“A’a Babu komai doctor daga barci ya tashi da wannan abun”.
Abubakar ya fada, yayin da Abba ya Kara da “kwarai kuwa muna zaune ya farka da wannan shivering din”.
Jinjina Kai doctor Omolen Yaya Yana faman gwaje-gwajensa, rubuta yayi a takarda ya Miko Yana fadin.
“Ayi maza a kawo wannan alluran yanzu za’ayi Masa”.
Habib ne ya karba ya nufi kofa,mahmud ne ya ya biyo shi da sauri suka fito, sun Fara tafiya mahmud yaga jikin Habib sai tsuma yake tamkar ze Fadi shima, rikeshi Habib yayi Yana fadin.
“Wallahi kaina juyawa yake yi”.
Ya fada Yana dafe Kansa.
“Haba Mana Habib take it easy, kada ka jawowa kanka wani problem din, zauna a Nan Ina zuwa”.
Ya nuna Masa wani Dan bencin a gefen baranda da sauri yayi gaba da takardar a hannunsa, maganar Abdul Hakeem yaji daga bayansa Yana fadin.
“Muje kawai Naga Habib ma Kamar Baya cikin nutsuwarsa”.
Tare suka jera har pharmacy suna tattaunawa Kan yanayin lalurar malam din.
Allurai biyu aka samu a cikin ukun Daya rubuta, a Nan pharmacy din suka fada musu dayar tana da wahalar samu sai dai su duba a manyan chemist cikin gari ko za’a dace, biyun suka Fara kaiwa suka fadawa doctor dayar babu amma zasu duba a cikin gari ko za’a samu, wani chemist ya fada musu yace suje in dai Babu a can su dawo kawai ba za’a samu ba a ko Ina.
Tare da Abdul Hakeem suka tafi shi yake driving din, sunje babu sun basu tabbacin sai dai a kano ko Bauchi.
Lokacin da suka dawo doctor Omolen suka samu shi kadai saura doctors din ya sallame su, shima Baba malam din ya Sami barci jijjigawa ta lafa.
Bayanin da masu chemist din sukayi musu suka fada masa, Abba ya kalla yace Yana son ganinsu a office.
Ya fita da sauri irin Basu na likitoci, Abba da mahmud da Abdul Hakeem sukabi doctor yayin da Habib da Abubakar suka rufawa doctor baya.
Ya rigasu shiga office din suna zuwa suka same shi a tsaye Yana kaiwa da kawawa, shigowar su yasa ya dakata ya nuna musu resting chairs na office din yace su zauna, bayani ya Fara musu Yana kallon Abba.
“Alhaji dole a samo wannan allurar yau ayi Masa Kuma yanda ka’idarta take dole Wanda za’a yiwa Yana kusa ma’ana ba’a fito da ita daga fridge har sai Wanda za’a yiwa Yana kusa Bata minti biyar a zafi zata lalace Dan haka dole mu turaku Kano ko Bauchi a yau din Nan saboda idan aka dauki lokaci ba’ayi Masa ita ba za’a shiga want condition din Kuma Wanda bama fata tunda Kansa ne ya bugu lokacin Daya samu tsautsayin munga casa din to munyi zaton minor case ne, saida hakan ta faru Kuma muka tabbatar da abinda muka gani, yanzu Shawara ta rage taku sai ku zabi Inda kuke ganin yafi dacewa sai ku tafi kafin visa din ku ta fito ana son ayi Masa wannan allurar Kamar sau hudu duk bayan Twelve hours are yinta” .
Kafin Abba ya samu zarafin magana mahmud yayi saurin fadin.
“Ina ganin doctor gara muje kanon tunda ta kanon zamu tashi, idan mukaje Bauchi Kamar mun koma baya kenan, ai kace ko gida za’a iya Zama indai akwai Wanda zeyi allurar?”
Kai ya gyada masa alamar tabbatarwa.
Abba ne yace “Mahmud Ina ganin Kamar abin zeyi muku yawa abin fa bana Wasa bane kana ganin su mutanen naku zasuyi abinda ya kamata? Dazu yaron Nan Sameer ya kirani yayi min bayanin komai har booking din Asibitin ya fada min ya gama komai Yana ganin daga nan zuwa gobe ko jibi za’a iya samun visa, ya fada min wait uwata Bata samu visa ba yaso ya hada da ita saboda lalurar ta, nace Masa ba komai hakan ma Allah ya saka muku da Alkhairi, na saka Masa wani Abu a account dinsa kafin na biyo ku muga abinda Hali yayi, yanzu ma Abdul Hakeem ze saka Mata kudi account dinka saboda wannan data taso”.
Godiya mahmud da Abdul Hakeem sukayi Masa sannan suka fito suka bar Abba da docy Yana Kara fada Masa irin yanda yanayin ciwon yake.
Har suka dawo dakin da Baba malam din ke ciki suna tattaunawa dai Kan fitar da za’ayi da baba malam din.
Suna zuwa Mahmud ya cewa Habib da Abubakar su maza su koma su shirya zasu wuce Kano yanzu su taho da Iya Abu, key din motar da mahmud yazo da ita ya mikawa Habib yace suje a ciki,sai bayan sun wuce ne Abba ya shigo tare da wasu manyan mutane suka jajanta musu jikin malam din tunda barci yake, kudi masu dama suka mikawa Abdul Hakeem suka fita suna masa fatan samun lafiya.
Malam Bala ne ya shigo da sauri ya mikawa Abba waya Yana fadin.
“Yallabai gashi Ina ganin bakin sun karaso gidan gonar”.
Wayar ya amsa yaga sune, kafin ya Kira an Kara Kira..
Dauka yayi ya amsa sallamar kafin ya Dora da fadin.
“Dan Allah ki jira Ina da patient ne a Asibiti”.
Ya kashe Kiran.
Mahmud ya duba Yana fadin.
“Mahmud Bari naje nayi Baki daga Abuja Wadanda zasuyi aikin titina da office dina ya kawo cikin gari da Kuma gyaran gadar jama’are, yanzu malam Bala ze dawo saiya kaiku kanon ya tayaku neman gurin Kwana kafin ku tafi sai kuyi amfani da wannan kudin idan Basu Isa ba kayi min magana kada kaji nauyi na Nima mahaifinka ne”.
Cikin ladabi Mahmud din yace.
“Nagode Abba Allah ya Kara sutura, basai Malam Balan ya dawo ba akwai motar da oga Sameer ya Bari jiya sai Habib ya tukamu a ciki kawai, Kuma akawai gidan da zamu zauna a Nan kusa da Asibitin malan Aminu kanon tunda doctor yace suna da allaurar a can”.
“To babu laifi Allah yayi Albarka yasa a Dace”
Su duka suka amsa da “Amin”.
Har gurin motar mahmud ya rako Abba, tare da Abdul Hakeem suka wuce saboda yawanci idan irin wannan project din yaso Abdul Hakeem keyi Masa monitoring na aikin.
Su Habib Basu Bata lokaci ba suka dawo da Iyayen jakunkuna take mahmud yace ba Wanda ze dauki kaya, Dan murmushi Abubakar yayi yasan za’a Rina babu yanda beyi da Habib akan kada su dauki Kaya yayi Masa musu Dan haka ya biye Masa suka dauko, tare sukazo da iya Abu, Mahmud ya gaisheta ya Kara jajanta Mata jikin malam, daidai saitin kansa taje ta tsaya tana kallonsa, Fara matse hawaye tayi tana fadin .
*Malam haka Allah yayi da Kai? Ubangiji ya baka lafiya idan na tafiya ya kaika da sa’a ya baka ikon cikawa da kalmatushshahada , na yafe maka duk abinda kayi min da gangan ki da gaske Allah ya yafe maka, saita fashe da kuka sosai, Habib ne ya janyota gefe Mahmud Kuma ya fita da ita Yana fadin.
“Kiyi hakuri cuta ita ke shiga Nan da Nan sauki sai a hankali, kici gaba da yi Masa Addu’a kawai ita yafi bukata a yanzu”.
Gefen hijabinta ta saka tana share hawayenta tana fadin.
*Kayya Dan nan malam sai abinda Allah yayi dubi fa yanda yake Sambal a kwance Kamar gawa ga want numfashi da yake da sauri da sauri “.
Sai wasu hawayen, bai Bari ta koma ciki ba key kawai yace Habib ya Miko Masa, ta tasata gaba suka bar Asibitin.
Har cikin parlourn ta Mahmud ya rakata shida Bilyaminu daya samu a kofar gidan Yana bawa wasu Yara wani aikin gyaran itacen da aka kawo Wanda ake musu girki dashi, sun Jima suna Bata Baki kafin ta hakura da kukan da take kudi mahmud ya aje mata Wanda har sukazo su taoratata, sannan yace .
“Ga Bilyaminu Nan shine zeci gaba da kula da komai na gidan duk abinda babu shi za’a tambaya Kuma idan mun Isa India Zan Kira shi ya ringa kawo Miki wayar kina ganin yanda jikin nasa yake”.
Godiya ta dunga Jero Masa da addu’ar fatan Alkhairi har suka fice.
Directly gidan su zahra ya wuce, magaji ya Nemo a waya yayi sa’a Yana gida yace ya fadawa Ammah ze shigo ya gaisheta.
Lokacin da suka shiga ciki,Mama na kofar main kitchen dinsu tana yiwa sahura magana, a mutunce mahmud ya gaisheta sahura ta garzayo ta gaishe shi, har suka shige part din Ammah kamshinsa Yana gurin da Ido Mama ta bisu. Saida suka bacewa ganinsu sannan sahura ta matso kusa da Mama tana fadin “Wai Mama Baki gane wannan yaron bane Naga kin bisu da kallo”.
Lemon da take Sha a cup ta kurba tana duban sahura.
“Ina fa na wani gane shi nasan ‘ya’yan manyan kasar Nan ne dubk yanda yake Mana ko Ina magaji ya samo shi Dan shishshigi har gurin uwa aka kawo shi to dai Babu ‘yar da za’a lika Masa Daya ce agola Kuma ta bige da yaron malam”.
Ta fada tana cigaba da Kora ruwan lemon ta.
“Mama Wai kina nufin Baki gane mijin Zahra bane ba?”.
Ai da fadin da kwarewar Mama ba’afi minti Daya ba, Nan da Nan sai tari Kamar zata sik’e da gudu sahura ta dauko Mata ruwan ta watsa gishiri a ciki ta Bata Tasha.
Magaji na gaba Mahmud na bayansa suka shiga parlourn Ammah, komai tsab ba abinda kakeji sai sanyi AC da sansanyan kamshin turaren wuta Mai Kama daki da freshner, gurin Zama magajin ya nuna Masa ya wuce corridor da ze sada shi da bedrooms dinta,a Kan carpet Mahmud ya zauna, tare da magajin suka fito Ammah tana sauko steps din tana Masa sallama.
Cikin nuna tsantsar girmamawa mahmud ya amsa sallamar Yana fadin.
“Barka fitowa Ammah”.
“Barka kadai , an shigo kenan ya wajen Mai jikin?”.Ta fada tana Zama a Dan nesa dashi.
Gaishe ta ya farayi sannan ya amsa Mata da.
“Mai jiki Alhamdulillahi, yanzu ma zuwa nayi nayi Miki sallama zamu wuce Kano dashi, jikin ne babu Dadi Kuma a Nan Basu da allurar Daya kamata ayi Masa shine zamu wuce yau Ina Jin gobe in dai visa ta Zama ready zamu wuce Indian in Sha Allah”.
Tunda ya Fara Kora Mata bayani take jinjina Kai daga ita sai Allahn Daya halicceta suka sa me take kissimawa a zuciyarta.
Cikin nuna alhinin abin Ammah yace..”Ikon Allah kowa da irin tasa kaddarar, Allah ya yayewa muslmi wahala yasa kaffararsa ce wannan”.
“Allahumma Amin”.
Mahmud ya fada, sai Kuma parlourn yayi tsit, ga magana a bakin Ammah amman sai taji yaron yayi Mata masifar kwarjini, yanda ta kare Masa kallo yau ita abin har tsoro ya Bata yanda ta ganshi, da ganinsa kasan ba mutumin banza bane.
Da gyara Zama Mahmud yayi ciki karfin Hali yace.
“Ammah gata Nan Dan Allah zata zauna a garin Nan Bata son Kano ko kadan naso tayi zamanta Amma ta nuna Bata so, sai su zauna da matar da sukaje Kano tare kafin muga abinda Allah zeyi akan lamarin, Kuma Dan Allah Ammah a kula da Wanda ze Bata Abu taci a cikin gidan nan in da hali ma ke kadai Zaki Bata Abu taci itama Matar a fada Mata ta kula kada kowa ya Bata Abu ta bawa zahra Dan Allah”.
Ita Ammah duk ya sakata a duhu, to meya kawo wannan maganar da gani har cikin zuciyarsa abinda ya fada, Bata zafafa ba tace.
“In Sha Allah za’a kula, Allah ya tsare”.
“Allahumma Amin”.
Ya fada Zama ya gyara, ganin haka yasa Ammah mikewa tana fadin.
“Ka Karasa tana wancan dakin ta nuna Masa da hannu tayi gaba wurin hanyar kitchen.
Cikin nutsuwa ya ratsa parlourn ya nufi bedroom din da Ammah ta nuna masa, a hankali ya Kama handle din kofar ya shiga, idonta a rufe da earpiece a kunnenta be Karasa Inda take ba jikin kofar ya jingina ya Zuba Mata idanun dake Bata tsoro a da.
A hankali scent dinsa ya shiga hancinta da sauri ta juyi Inda take jiyo shi carab idanunsu ya sarke, tashi tayi zaune da sauri tana rarraba sexy eyes dinta.
Hannuwa ya bude Mata alamun ta taso ta tazo gurinsa.
Ita fa tsoro ne ya kamata kada fa Aljani yayi siffarsa ya biyo ta, to ta Ina ma ze shigo har nan.
Wani killer smile yayi mata.
“Kina mamakin yanda akayi na shigo ko? To Ammah ta turoni nazo na samu lada”.
Dan turo baki tayi irin na shagwababbun yaran nan.
“Wallahi ka bani tsoro, ta Ina ka shigo Nan? Ina Ammah?”.
Takowa yayi a hankali ya karaso Inda take ya zauna very close to her ya cire Mata dayan earpiece din daga kunnenta.
“Ki daina sakawa Yana damage din ear drum na kunne kinji kada ki tashi hankalina, yanzu ki taso mu tafi Kano zamu wuce da Baba malam daga can Kuma zamu wuce Indian din, naso mu tafi tare to duk iya kokari Sameer yayi Amma abun yaki yuwuwa, taso muje kiji dani”.
Ya fada Yana kwantar da Kansa a jikin wuyanta,ya saka hannu ya tallabo fuskarta ya hade bakinsu, da sauri ta janye tana nuna Masa kofa tana fadin.
“Ammahhhh…”
“Da saninta na shigo ba satar guri nayi ba, taso muje lokaci Yana tafiya”.
Narai narai tayi da ido.
“Dan Allah ka barni na zauna a Nan wallahi tsoron gidan nan nakeyi yayi min girma ga unguwar babu mutane da yawa”.
Tashi yayi ya nufi kofa Yana Fadin.
“Ina jiranki a parlour ya fice, har lokacin ba kowa sai kayan Abinci da fruits a Kan table mat a tsakiyar parlourn.
Zahra ce ta fito tana Dan gyara rolling din kanta bedroom din Ammah ta nufa ta fito da handbag dinta ta wuce ta nufi kitchen inda ta samu Alawiyya tana aiki.
“Ina Ammah?”.
Zahra ta tambayeta.
“Tana bangaren Abba zata dauko sakon Daya turo a daukar masa, tana Nan Ammah ta shigo da takardu ta mikawa Alawiyya ta kaiwa malam Bala driver.
. lokacin da suka fito zahra nata zabgawa Ammah magiyar da besan kota mecece ba, zahra Ammah ta kalla.
“Ya haka Baki bashi abincin bane?”.
Dan narke fuska tayi.
“Ni ai bansan na waye ba, a Nan na gani kawai na dauka Baki zakiyi”.
Harara Ammah ta zabga mata.
“Amma ke bansan yaushe Zaki nutsu ba wallahi to maza Zuba Masa shida zeyi tafiya”.
“A’a Ammah zamu tafi dashi can kada na makara”.
Mahmud ya fada Yana kokarin tashi.
“To shike nan Bari Alawiyya ta Kai muku mota, maza fada Mata ta dauko basket ta Zuba”.
Kitchen din zahra ta koma, Ammah Kuma ta fuskanci Mahmud dake fadin.
“Zamu tafi Ammah kiyi min addu’a”.
Sai taji yaron ya Kara shiga ranta duk Inda ya fito ya samu uwa ta gari, cikin nuna kauna tace Masa.
“Ubangiji yayi Albarka ya taimaka ya kaiku lafiya ya bada abinda akaje nema”.
” Allahumma Amin, nagode”.
Ya tashi yayi waje, Yana fita zahra ta matso kusa da Ammah.
“Yanzu Ammah ki rokar min ko sati Daya ya Bari nayi Amma kika Kiya shikenan”.
“Kina son na Zama uwar banza kenan? yaron Nan bansan abinda ya gano ba tunda harya iya tunkarata da irin maganar Daya fada min kije kawai ki yiwa mijinki biyayya idan anjima da magariba magaji ze kawo zilan sai ku zauna, kije Yana jiranki kada ya kosa”.
Tare suka fito da Alawiyya data dauko Abinci.
Tunda suka dauki hanya yake amsa waya da alama da likita yake magana a yanayin yanda ta fuskanta.
Lokacin da suka shiga gidan wani daban ta gani ba zayyan ba sai safwan tunda shi tasan shi a kano.
Gurin motar suka karaso, da sauri safwan ya bude masa ya fito.
Dayan ya duba yace.
“Naseer ka kula da gidan Nan kafin zayyan ya dawo idan an Jima wani yaro ze kawo wata mata, daga su ban amince wani ya shigo gidan nan ba har zayyan ya dawo, sannan ya juya gurin safwan ka Zama ready Zan fito Nan da ten minutes in Sha Allah”.
“To suka amsa sannan suka koma Inda suke.
Dayan side din mahmud ya koma ya bude Mata ta fito a yangace Yana nazarce da ita ba haka taso ba so tayi a ajeta a can ta Zama nama shi Kuma abinda bazeyi tolerating ba kenan.
Ta baya yabi da ita tayi mamakin ganin kofar kenan ginin dai sak irin na Kano ne, suna wuce idanun jama’a ta dauketa cak Bai direta a ko Ina ba sai bedroom dinsu ya ajeta, wata irin soyayya ya kwada Mata Mai wuyar mantawa tare sukayi wanka shaf-shaf suka suka shirya da kyar ta matsa Masa yaci abincin, Yana mak’ale da ita suka fito, cikin motar suka shiga tare a Nan ma saida yayi son ransa kafin ya barta ta fito.
Saida ta juya ta Fara tafiya sannan safwan ya taso, fitowa mahmud din yayi.
“Precious….”
Ya fada Yana Jan sunan.
Cak ta tsaya Amma Bata juyo ba Dan idanunta fal da hawaye ji take Kamar ta bishi su tafi Batasan tayi mugun sabo dashi Kamar haka ba sai yanzu da zeyi Mata nisa, Saida ta shanye hawayen sannan ta juyo, wani kiss yayi Mata blowing dinsa sannan yace.
“I missed you my previous, I really missed you”.
“And me too….” Ta fada tana shigewa ciki.
Jikinsa ba karamin sanyi yayi ba a haka suka fice daga gidan.

,

Mahmud Basu shiga Kano ba sai kusan magariba sultan road suka nufa, Saida ya huta yayi wanka sannan ya kirawo Sameer ya fada Masa ya shigo yazo ya sameshi a sultan road, ta Tarauni suka biya suka sai musu fruits sannan suka wuce can court road din.

Ku Cigaba da bibiyan shafinmu domin samun fitattun littafai.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button