An Bude Sabon Shirin Bada Tallafin Kudi Ga Mutanen Karkara Mai Suna (NWAP)

Kungiyar Mata Manoma ta Najeriya (NWAP) national rural woman in agric program ta yi kira ga shugaban kasa Bola Tinubu da mambobin majalisar ministocinsa da su sanya matan karkara a matsayin wadanda za su ci gajiyar ayyukan noma ga manoma a Najeriya.

Omolara Svensson, kodinetan kungiyar na kasa ne ya yi wannan kiran yayin da take magana a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ranar Laraba.

Ta nuna rashin gamsuwa da yadda gwamnatin tarayya ta yi watsi da ayyukan noma ga mata manoma. Svensson ya bayyana cewa galibin ayyukan noma an yi su ne ga manoman birane, duk da cewa sun gudanar da ayyukan noma kadan idan aka kwatanta da manoman yankunan karkara.

A yanzu haka de an fitar da sabon shirin da za a bawa matan karkara da za a bawa tallafin kudi domin inganta ayyukan nomansu.

Kamar yadda akayi shirin RRR shima wannan haka yake domin kuwa ana danna wasu lambobine domin shiga cikin shirin,  ko muce domin cika neman tallafin

Masu bukatar cikawa Matansu ko kannensu ga Yadda zakuyi.

Da farko zaku danna Wannan lambobin
*347*781#

Bayan kun danna Lambar zai kawo muku inda zaku sanya Full name dinku saiku sanya

Daga nan zai kawoku wajen sanya number waya

Daga nan sai wajen jiha

Sai wajen Local government

Sai wajen sanya word wato unguwar ka

Sai wajen sanya Pin saika kirkiri number guda 4 saika sanya

Sannan sai wajen sanya Sunan noman da kakeyi nanma saika sanya.

Daga nan zai tambayeka shin ka amince ayi save na bayanan daga shigar? Saika danna ka amince.

Daga nan shikkenan zasu baka wasu code wato Application ID sai kayi screenshoot dinsu koka rubucesu domin sune shedar ka cika wannan tallafin.

Allah ya bada sa’a

Note: Wannan shirin 70% na matan karkarane dan haka bai zama lalle idan kana namiji ka cika kuma ka samuba,  amma duk da hakan zaka iya cikawa domin ba asan inda rabon yakeba.

Allah ya bamu sa’a

Join Our Whatsapp Group

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button