Ajiya A Duhu Littafi Na Biyu (2)

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com

Ajiya A Duhu Book 2

Related Articles

Page 18

Sosai jinin jikinsa ya shiga wani irin harmutsawa har cikin brain ɗinsa, illahirin ƙofofin gashinsa suka shiga bubbuɗewa. Domin al’amarin yazo masa da wani irin girma na gaske sakamakon abinda ya ɗauki tsawon shekaru yana dannewa da tsiya-tsiya. Tsaf ya kanainaye Hajiya Maanalu ta yanda bata da damar yin wani yinƙuri koda na motsa kanta ne. Sumbatarta yake cikin rikicewar yanayi da birkicewar tunani, sai dai hakan bai sakashi kasancewa a rashin nutsuwar da ALLAH ya azurtashi da ita ba. Akowane irin yanayi AA nutsatstsen mutum ne mai cike da kamala da dattako, nutsuwa akan komai halittar AA ce, sannan a cikin jinin jikinsa take. Matuƙar nisan kiwo ƙwaƙwalwarsa da zuciyarsa suka tafi ya manta da inda suke, dan kuwa tuni ya fara ƙoƙarin warware mata veil ɗin jikinta da take ta ƙoƙarin ganin ta riƙe ta hanashi hakan, amma yanda ya matseta a cikin kujerar hakan ya gagara, har ALLAH ya bashi nasarar yakicesa ya tura hannunsa a bayanta ya fara kici-kicin sauke zip ɗin bayan rigarta. Zuwa yanzu kam matuƙar ƙololuwar tashin hankali da birkicewar zuciya Maanal ta shiga. Dan tsabar tsoro da firgici zuciyarta neman buɗewa take gida biyu. Abu biyu ne ke maimaita kansu a ƙwaƙwalwarta a wannan gaɓar. Tsoro mai tsananin gaske, da flash back na wasu shekaru da suka shuɗe a rayuwarsu, sai dai tarihin irin wannan gaɓar bazai taɓa gogewa ba har abada dan tabone da ya riga yay tammbari a RAYUWARSU na har abada. A hankali ta saki masa wani irin kuka da kaima bayansa duka dan ta fahimci kamar ya manta itace fa Bestyn sa. Sai dai babu alamar yasan tanayi dan har yayi nasarar sauke zip ɗin yakai ga hook ɗin b ɗinta yana kici-kicin ciresu suma… A dai-dai nan kira ya shigo cikin wayarsa, kiran daya saka komai tsayawa cak harda fitar numfashinsu. Bawai kiran ne yay tasiri ba ga AA, a’a sautin dake tabbatar masa da kiran daga waye ne ya tasirantu a garesa matuƙa. Yafi sakan goma bai iya ya motsa ba balle janye jikinsa kafin ya zare lips ɗinsa akan nata a hankali, sai dai ya kasa raba jikinsa a nata saima sake ƙanƙameta da yay na fin sakan ashirin. A lokacin daya ja jikin nasa baya ya koma a nasa mazaunin jagwab ne ya bama Maanal damar cusa kanta a cikin ƙafafunta ta ƙanƙame jikinta waje guda gaba ɗaya. Jikin nata kuma sai wani kalar rawa yake na tsorata da shiga firgici ga kunya mai tsananin gaske da bata taɓa shiga tsakaninta da shi ba a rayuwarta. Zuciyarta kuwa babu abinda take sai rabewa da komawa ta tsuke kanta da kanta….
Kiran Abah daya sake shigo masa ne ya sashi ɗaukar ruwan dake gefen sa ya ɓalle murfin ya shiga kwankwaɗa duk da uban zafin da yake da shi. Shi kansa ma bai san tun yaushe ruwan yake a motar ba. Sai da yasha kusan rabi ya kife kansa a steering yana maida numfashi, a karo na uku kiran Abahn ya sake shigowa. Sai yanzu ne ya sami damar dai-daita kansa da ƙyar ya ɗaga wayar.
“Ajwaad! Kana kallon ƙarfe nawa kuwa? Sai ɗaya tayi zaku dawo?”. Nutsatstsiyar muryar Abah ta daki cikin kunnensa. Idanunsa ya sake lumshewa ya buɗe da ƙyar, cikin ƙoƙarin ganin muryarsa ta kuma samun nutsuwa yay ɗan gyaran maƙoshi kafin ƙasa-ƙasa ya ce, “Gamu nan in sha ALLAHU Abah”.
Shiru Abah yay sautin shaƙaƙƙiyar muryar ta AA na dakar masa zuciya. Dan duk wanda ya sanshi ya jisa a yanzu zai fahimci akwai lauje cikin naɗi. Amma kasancewarsa dattijon arziƙi sai cewa yay, “Okay kuyi sauri Oum ɗinku nason kwanciya” daga haka ya yanke kiran. Idanu AA ya sake lumshewa ya buɗe a karo na barkatai, shi kansa ganin ƙarfe nawa sai da yaji zuciyarsa ta girgiza. Harga ALLAH bai san sun jima haka ba, dan sai yake ganin ma kamar basu wuce minti talatin da fitowar ba. A karo na farko ya maida birkitattun idanunsa kan Maanal dake a duƙufe har yanzu. Lallausar fatar bayanta da hasken fitilar titin ta hasko ya zubama idanu, sai farar b ɗin jikinta datai matuƙar dacewa da fatar gata fes babu wani alamar datti a tare da ita. Numfashi ya sake ja a fisge, kafin cike da kasala ya kai hannu kan zip ɗin zai ja mata shi saman. Zaram ta miƙe zaune sosai idanunta share-share da hawaye. Shi dariya ma taso bashi ganin yanda ta wani zazzaro masa idanun alamar gargaɗi. Ƙasan zuciyarsa kuwa sai yaji kamar yana jin nauyinta shima musamman da wani gefe na zuciyar keta maimaita masa kalmar (Bestynka ce fa! Amma ka rufe ido ka aikata mata wannan abin kunyar har kana neman sakin layi) kauda tunanin yay gefe murmushin gefen baki na neman suɓuce masa. Amma sai ya daure a tausashe ya ce, “Yi haƙuri zip ɗin zan rufe miki, idan kuma kina son Abanki ya gane to a barshi a hakan kawai kinga na huta sai yace mu wuce sashen mu kawai ya salllama”. Ai da gudun tsiya ta duƙe alamar ya rufe matan. Yanzu kam saida ya murmusa kaɗan, kafin ya kai hannun yaja zip ɗin, yazo dai-dai jikin b ɗin ta ya dakata, hook ɗin yay ƙoƙarin maida mata dan duk ya ciresu saura ɗaya jal ya rage masa. Rumtse idanu kawai Maanal tayi da ƙarfin tsiya harya kammala ya ƙarasa ja mata zip ɗin.
“Oya wanke fuska mu wuce, idan kuma a samu hotel anan kusa muƙarasa to”.
A baima gama rufe baki ba ta ɓalle murfin motar, batare data kallesa ba ta warce goran ruwan hannunsa ta juya ta fara wanke fuskanta. Murmushi ya saki, tare da kai hannu ya shafa lallausar sumar kansa dake lashe kuɗaɗe da shima bai san adadi ba. Koda ta gama bata kallesa ba, ta yarda goran a ƙasa ta maida murfin ta rufo, sai kuma ta matsa jikin murfin ta maƙure. Komai baice mata ba, sai handkacheff ɗinsa mai ƙamshi ya miƙa mata kawai. Ɗan kallonsa tayi, suka ko haɗa ido. Da sauri ta janye nata tana fisgar handky ɗin kawai. Nanma murmushi yay yayima motar key suka cigaba da tafiya. Sai dai yanzu gudu yake sosai saɓanin ɗazun. Cikin ƙanƙanin lokaci kuwa sai gasu a gaban ƙaton gate ɗin gidansu…

Koda suka nufi sashen Oum salaf-salaf Maanal ke tafiya kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki. Gani take kamar tana shiga kowa zai gane abinda ya faru a tsakaninsu. Musamman ma Abah da Oum. Ɗan tsayawa AA yayi, ita kuma kanta a ƙasa tunanin da take yi ya ɗauke dukkan hankalinta har tazo gab da shi bata sani ba. Sai da ta bugu da bayansa sannan ta ɗago da sauri, tayi baya kuma zata faɗi. Saurin juyowa yay tare da riƙota a lokaci guda, cike da kulawa ya jinginata da jikin bango. Muryarsa a sanyaye saboda halin da yake ciki ya riƙe fuskarta, ɗayan hannunta kuma a cikin nashi yana kallon fuskar ya ce, “Tunanin mi kikeyi ne haka?”.
Wata irin kunyarsa take ji shima, dan haka tana ɗan ɗago idonta ta kallai ta maida su ta risinar, shiko nashi yawo kawai suke akan ƙyaƙyƙyawar fiskarta. Kanta kawai ta girgiza masa tana ƙoƙarin janye hannunta dake a cikin nasa yaƙi bata damar hakan. Hawayen da take riƙewane suka ziraro, ya waro lumsassun nasa sosai. “Ya arrahaman, miye abin kukan kuma?”.
Cikin rawar murya ta ce, “Yanzu idan Oum da Abah suka gane fa”.
Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya sauke, a ransa yana faɗin, (Ashefa na manta yarinyar nan ɗanya ce, rinton aji yasata gama makaranta da wuri) a fili kam sai ya shafa fiskarta tare da faɗin, “Sai dai in kece kika so su gane”. Kallonsa ta ɗago tayi sosai a karo na farko, ya jinjina mata kansa yana ɗan laɓe baki da murmushin gefen baki a tare. Sai kuma ya shafa kanta cike da lallashi da tsokana ya rankwafa yana mai kai bakinsa saitin kunnenta da raɗa ya ce, “To ko mu tafi sashen mu kawai ki kwana acan, da asuba na miki alƙawarinkin rakoki da wuri kafin kowa ya tashi”.
Tamkar wadda ya zaburar, ta sa hannayenta duka biyu a ƙitjinsa ta tura shi baya. Matsawar yayi yana dariya, ita ko ta kwasa da ɗan gudu cikin sashen Oum. Ko ganin Abah dake bayansu ma batayi ba sam. A falon kuwa akwai Oum, Mamy, Nibras, Saheeba da Fawzan harda babban Yaya a yanzu na zaune suna hira sai kawai ganinta sukai kamar walƙiya ta wuce hanyar upstairs. Da sauri Oum ta ce, “Munga idi Baby waya biyoki haka?”.
“Oum fitsari-fitsari” ta faɗa batare data waiwayo ba. Dan tasan wannan dabararce kawai zata rabata da jin kunya. Saboda babu wanda zai kalleta bai fahimci wani abu ba a fuskar ta da lips ɗinta da yasha wahala a hannun wancan mutumin. Dariya Fawzan da Babban Yaya suka saki a lokaci guda, dan abinda Maanal ɗin tayi ya tuna musu da baya ne. Haka take yi idan suka dawo makaranta, sai ta riƙe fitsari tun daga can, mota na tsayawa ta fita a guje zuwa ciki tana faɗin, “Fitsari-fitsari”. Sai da Ammie ta zaneta wataran aka samu lafiya ta daina abin nan. Oum ma dai dariyar tayi, dan itama dai abinda yazo mata a rai kenan. Mamy da su Saheeba kam wani irin takaici ne ya ƙullesu, da kallon abinda Maanal ɗin tayi matsayin wani sabon bariki….

A waje kam, AA na gama dariyarsa dake fita a hankali ya juyo da nufin shigewa shima sukai ido huɗu da Abah daya harɗe hannaye a ƙirji ya tsaresa da idanu. Da sauri AA ya juya yana rumtse idanu da kai hannu ya shafa kansa, haƙoransa damtse da lips ɗinsa. A zuciyarsa faɗi yake (Ajwaad kaga takanka, tsohon nan ba raga maka zai yi ba….) katsewa zancen zucin nasa yay saboda taɓashi da akayi, juyowa yay kansa a ƙasa hannunsa a cikin sumar kansa, sai kuma ya ɗan buɗe ido ɗaya ya ɗan kalla Abahn. Abah da dariya ke cinsa a rai ya gimtse da ƙyar ya wani sake tsatsatsaresa da idanun. Sai AA ɗin cayay, “La Abah kai ne?”.
“A’a bani bane aljani ne”.
Abah ya bashi amsa cike da gatse. Bayansa AA ya koma ya tungumesa, ya tabbatar hakan shine rufun asirinsa dan wlhy tsaf Abah zai gane halin da yake ciki, musamman idanunsa da suka kaɗe. Cike da shagwaɓa ya kwantar da kansa a kafaɗar Aban yana faɗin, “Kaga ko Abah ALLAH ban lura time ya tafi haka ba. Na tuba! Na tuba! Na tuba!!”.
Yanzu kam kasa daurewa Abah yay saida ya murmusa. Amma kasancewar AA na bayansa ba gani yay ba. Fuskar ya maida ya himtse a dake ya ce, “Ai na faɗa maka daman saina ƙara kwanakin suspension idan ka daɗe min da yarinya”.
A sanyaye AA ya ce, “Abah holdup ne fa a hanyar”.
“Na aljanu ko? Yo in ba na aljanu ba a daren nan wane huldup ne zai taru. Kaji tsoron ALLAH Ajwaad”.
Ƙaramar dariya yanzu kam AA ɗin yayi da faɗin, “To Abah kawai abar kaza mana cikin gashinta. Kawai kayi murna mun dawo bamu ɓata ba ma”.
Rankwashi Abah ya kai masa bisa kai, da sauri ya sakesa ya shige sashen Oum yana dariya. Shima Aban dariya yake yi da girgiza kansa. Wani irin farin ciki na ratsa masa zuciya. Rabon da yaga Ajwaad a irin wannan yanayin na farin cikin da har zai dinga wasa da dariya kai tsaye an ɗauki shekaru masu yawa. Ko tsokanarsa sukai sai dai yay guntun murmushi kawai yay shiru. Amma yau jiba yanda yake zuba masa surutu da shagwaɓa kai tsaye. Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya nufi sashensa yana mai jerama UBANGIJI kirari da godiya.

Abah namu, anya! Anya kuwa. Bara dai nayi shiru

Ku biyomu domin karanta cigaba.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button