‘Yan Ashawo Romantic Story:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com

Page7️⃣&8️⃣

Related Articles

Saida ranar hantsi ya daki dutsen da take kai yasata farkawa saboda zafi da ya ɗauka ,ga wani ƙwallelen ranar dake dukanta tashi tayi da sauri sai sannan ta kalli ƙafarta taga duk ta tattaka ƙaya garin gudun ƙwatan rai duk yayi jini ,gangarawa tayi ƙarƙashin wani bishiya mara wadatan ganyaye sai ƙayoyi barkatai a jiki ,haka ta samu guri ta share ta zauna tana cire ƙayoyin ƙafarta hawaye na gangaro mata a fuska ,ga yunwa tanaji ,ga damuwar rashin mafaka ga damuwar rashin iyaye ,ƙaran babbar mota taji ɓiyyyy! Wanda saida ya tsorata ta don a iya yawon tallan nononta batasan wani abu waishi motaba sundai saba ganin jakuna akai ake aza kaya ,firgicewa tayi ta danna a na kare ,gudu takeyi tana ƙarajin hayaniyar motoci na ƙaruwa ,in taji horn ɗin mota ta nan hanyar saita kwasa tanan a furgice ,saitayi gudu sosai sai ta ƙara jin wani horn ɗin haka zata canja hanya ta cigaba da gudu ,ta wani fili ta shiga ,duwarwatsu irin wanda kowani ɗaya yayi girman gida , saƙawa tayi ta cikin duwatsun ta shiga filin sosai filine na dandaɓaryan jar ƙasa ta tafi iya ganinka amma a share tartar kamar tsakar gidan ƙauye da ake sharewa kullum ,kukan birai ta ringaji daga saman dutsen ,ɗaga kanta tayi a hankali taga birai ne kusan guda bakwai ,ɗaura hannu tayi aka “Shikenan wannan wani irin jejine na kawo kaina ?” Tsorone taji ya fara shigarta a hankali taji kamar ana cewa ke zo muyi wasa “
Da sauri ta juya bayanta ,wata yarinya ta gani bata wuce shekaru biyu ba da ƙaton kanta dakitso ƙwala ɗaya jal a tsakiyan ka ,haƙoran bakinta guda biyu ,mamakine ya kamata na ɗaya ina iyayen yarinyar nan sukene? Ya akayi ta iya magana irin na manya amma gata yarinya ƙarama? Ya akayi daga tsayawarta taga yarinyar ta ina ta fito?

Tsinke tunaninta tayi saboda yarinyar da ta miƙo mata tukunyar jar ƙasa ,da tandan waina shima na ƙasa “Kizo muyi wasa”

Duƙawa tayi ta dafa kafaɗun yarinyar da fillanci ta soma yi mata magana “ke Ina iyayenki suke da suka barki a wannan bahagon jejin” nuna mata arewa dasu tayi alamun suna can ,masifa Jiɗɗo ta shigayi “Gaskiya iyaye basu kyautawa yaransu ,uje in kaiki kuma in masu fada su bar sakinki kar namun daji su cinye ki ko maciji ya sare ki” zungwui zungwui suka ringa tafiya har suka fito bakin titi ,ga kwalta ya shimfiɗu Tata iya ganinka ,tsorone ya kama jiɗɗo a hankali ta waigo da nufin tace mata har yanzu ba’a kawo ba ? Ɓat ta nema yarinya ta ɓace “Ke er wada kina Ina???” Jiɗɗo ta shiga kiran er aljanar da ta raɗa mata er wada ,Amma ba amsa ,zata sake magana taga birran nan da suka maƙalƙale akan duwatsu sun firfuto mazansu suna tafe kaciyarsu ta fito waje jajazir ,da gudu suka tunkaro jiɗɗo

Habawa dafa ƙasa tayi tace ƙafa me naci ban baki ba ,ta fara shanye titin nan da gudu ,haka motoci suke giggiftawa lokaci bayan lokaci ƙwalwar Jiɗɗo ne ya birkice ga tsoron mota da takeji ga birrai da suke Binta

kanta birkicewa yayi ta fara jin jiri na kwasarta ,daidai nan motar nazeefa da Dauda yazo giftawa ,Tundaga nesa nazeefa tacema Dauda yayi slow down ,budurwan bafullatana irin na ƙurgurmin jejin nan tana gudu da alamun firgicewa “Malam Dauda bi mun ita ,waccan yarinyar ba a hayyacinta take ba ” Binta suka ringayi da mota itakuma tana ihu tana ƙara cin gudu wasu motocin na wucesu fuifuifui

Shan gabanta malam Dauda yayi da sauri suka fito ta kuwa juya baya ta sake dannawa a guje saidai cak ta tsaya ganin yarinyar nan tana mata dariya tana miƙo mata tandan yanɓu ,zubewa tayi akan gwuiwarta ta yanka ihu “Wayyo innawuro na Haukace …” Da sauri Nazeefa ta je ta kamota ,bata duba zarni da warin da takeyi ba haka ta ƙanƙameta tana tofa mata ayatul kursiy ,fiffuzga takeyi tana kusakeni ga biran nan tsirara zasuyi mun fyade ,gatanan tana kirana inzo muyi wasa wayyo Allah” gabaɗaya basu gane Hausar nata saboda yanda yike ingausa fillanci da hausa ga hausan ma baya fita sosai ,wawwaigawa Dauda yayi baiga kowa ba ,kana ya kalli Nazeefa “Hajiya jejin nan akwai haɗari gaya tsayuwar mu a cikinta “
Topa mata addu’ar ta sake yi a fuska sannan ta umurce ta ta buɗe idonta “kina ganinsu?” Buɗe idon tayi kawai tai arba da yarinyar tana daga gefe tana ƙyalƙyale mata da dariya ,kwantsama ihu tayi “wayyo gatanan tana mun dariya ” Tsorone ya kama Nazeefa da sauri ta girgiza jiɗɗo da ƙarfi “ke ina iyayenki suke ina ne rugarku ?”

“Sun kashemun Babawuro , innawuro da addata ,sun ƙona jejin mu sun gudu da garkenmu Ni kaɗai na tsira” ta fashe da wani kuka mai ban tausayi ,dukda tana masu kallon wasu halittu na dabam amma tasan mutanene jinsin ta

Miƙar da ita tayi ta jata zuwa motarsu nan ake shan dirga ita lallai bazata shiga wannan abunba ƙilama suje su yankata ,dama ance masu satan shanu mutanene en Maraya masu karatun boko suna ci da biro suna sace shanayen hilani ,tsaki Malam Dauda yayi musamman da ya gane itaɗin victim ce ,Kenan a kowani lokaci en bindigan zasu iya ritsasu ,da ƙarfi ya cicciɓeta ya cusa a mota ya ɓamo ƙofar bam ,Nazeefa ma ta shige gaban yaja motar da gudu suka bar hanyar da gudun ƙarshe
Waigawa tayi ta kalli jiɗɗo daketa faman wuwwurga ido bakinta ya bushe ƙamas kai ba sai an tambayeka tana fama da ƙishirwa ba da yunwa ɗakko goran ruwa tayi ta miƙa mata aikuwa da sauri ta karɓa ta kafa kai ta kwamkwaɗe kafin ta riƙe ciki saboda yanda cikinta ya murɗe ,suna daf da shiga gari suka tsaya a wani asibitin kan hanya suka miƙa ta da sauri aka saka mata ruwa ,Nurses’ sukayi mata bedbathing, suka wanke mata gashin kanta suka saka mata kayan asibiti duk wannan bidirin tana barci ,saboda a cikin maganin da aka bata harda anti anxiolytic kuma yina saka barci ,saboda a samu ta daina firgita .

Nazeefa gida suka wuce da malam Dauda ranta duk a dagule ta daɗe rabon da taga abun ban tausayi irin na jiɗɗo,Nigeria ƙasar mu na gado talaka yina cikin wani hali kullum suna mutuwa gomnati ma basu sani ba.


Tahreem saida ta gama da Iron lady ta mata transfer ɗin kuɗi masu nauyi a account sannan ta tuƙo motarta ta dawo gida ,lokacin anata kiran magriba ,tana shigowa taga kaf en matan gidan suna zaune sunata kallo wasu na buga karta wasu na shan shisha ,Tana sako ƙafa duk suka miƙe suna mata sannu da zuwa ,kallon talatu tayi da take zaune take zuƙar shisha hayaƙi ta hanci da baki da kunne , aikuwa ta cillo mata car key ɗin hannunta sannan ta ɗaura da masifa “kina haukane zan shigo gida bazakizo ki mun sannu da zuwa ba ? Wai ma dakata uban me kuke yi ana sallah duk kuna zaune ,so kuke fushin Allah ya kamani ,samuna ya fara ƙasa? Ina Nazeefa? “

A hankali talatu tace tana sama tunda ta dawo bata zauna a cikin mu ba “
“Ok ko naji nasan in tana nan dole ta saku kuyi sallah ,balaman banza balaman hofi ,da an barku a ƙauyenku da duk yanzu yaranku uku² ,to bazan ɗauki iskanci ba Ni a tafiyana ba ƙin yin ibada saboda ina tsoron Allah…..” Ta wuce fuuuu talatu na biye da ita da makullin hannunta

Tana ankare da tana take mata baya ,saida ta taka step ta riƙe ƙarfen ta jiyo cikeda masifa “meye kike bina ? Ko an aiko ki ki taken inuwa ne ,eye jikan Alya mayya?!” A sanyaye ta kalleta da jajayen Idanuwarta “Makullin motarki zan baki ” tayi magana tana miƙa mata makullin ,warcewa tayi ta haye sama tana sababin kar ta fito taga kowa a falon nan ,murɗa ƙofar tayi ta shiga ɗakin Nazeefa tana zaune akan darduma ta idar da sallah hannunta a sama tana addu’a tana kuka

Gaban Tahreem ne kawai taji ya faɗi dukda batasan dalilin hakan ba
“Nazee kin dawo ?” Shafa addu’ar tayi a hankali ta waigo ta kalleta “Na dawo uwarɗakina “
Haɗe fuska tayi “Wai sai yaushe zaki daina isana da kukan nan na banza da wofi ,wai wanine ya aikeki shigowa bariki?” A sanyaye tace “kiyi haƙuri wannan kukan na dolene ,Anty ko ke kika ga abunda na gani a yanda na sanki sai kinyi kukan da yafi nawa”
Katseta tayi cikin gwasalewa da nuna halin ko In kula “Ina en matan da kikaje samowa ?”
“Anty ban samo ba ,wallahi ance duk an turasu aikatau…!”

Tsawa ta daka mata sannan ta fara magana kamar za tayi kuka “shikenan kinaso kiyi mun ta leƙo ta koma,yanzu lokacin zaɓe yayi gari zai fara jiƙewa da kuɗi mai guntun sha’awa ma yinajin aljihunsa ya cika da kudi neman matan harka zaiyi ,shine kike so kimun baƙin ciki?…Haba nazee tunda na saki a matsayin PA ɗita business ɗina ya soma rawa , Innalillahi wainnailaihir rajiun ,to yanzu da kikaje kika dawo guzurin uwar me kika dawo mun dashi ko sai kukan iska?”

“Aunty wallahi kukana bashida alaka da zamana dake,a hanyane na haɗu da wata miskiniyar bafullatana ,ta rasa uwanta da ubanta da kowa nata,shine na taimaketa na fiddota daga daji yanzu haka tana asibiti ‘”

Tsaki taja ta juya tai ficewarta tana mata magana cikin gatsali da izgilanci “Allah ya baki lada ya sayyada,amma tabbas na soma gajiya da ciyar daku matuƙar kwalliya bata biyan kudin sabulu shara zanyi in rage en iskan can da basu da farinjinin anini sai shaye²n tsiya…

Ku Cigaba da bibiyanmu domin samun fitattun littafai masu kayatarwa.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button