Ya Abin Yake

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com
Page 42-43
a can gida bayan sunci abinci jamila taxaunar da salma tai tamata fada me ratsa jiki,inkaga salma xakace taji amma ina kwantan bauna kawai tai mata
Dan ita bata so wani yadhiga fadan ta da sameer ita kadai ta isa riga da wando.
Dara na suka shiga suka tsara girkin su me rai da lpy suka ci nasu suka bar na sameer a dinning din,wanke kwanu kan da suka bata sukai kafin suka nufi daki.
hira suke amma rabin hiran jan hankali akema salman,xuwa can aka.kira jamila a waya dauka tai cikin sauri suka fara magana.
Tsam salma tamike ta nufi parlor direct in da abincin sameer yake tanufa,budewa tai tasaki wa mugun murmushi wanda ya bani tsoro,rober gishiri ta jawo ta cika murfin rober ta juye a fride rice din ta kara rabin shi ta juye,jujjuya abin cin tai yay kaman haka aka xuba.
Kakkabe hannu wan ta tai tanu daki,kana dariya a xuciyar ta.
“Yaw xan ga inda xakaci abinci sai dai aje aci a waje amma ka gama cin abincin gidan nan “
Tura kofar tai har xuwa lkc jamila nata waya dagani kasan da masoyin ta take waya sai wani narkewa take kamar tana gabanshi.
“Umm shi mutum kullum waya dai waya dai sai kace kan ku aka fara soyayya ?”
Ita gamila bata masan tana yiba bare ta kula ta.
1saura sameer yadawo,saboda ya kasa xama a tashi saka makon yun war daya keji ta adda beshi.
Kaya kawai ya canxa ya fito lkc dukan su suna babban parlor xaune, kan dinning ya nufa ganin abin ci yasa yaji wani sanyi a ransa duk da yasan aykin jamilane.
Budewa yay yaxuba abincin a plate jikin shi har rawa yake sabo da yunwa.
spoon daya yakai ya tauna sai jiyay komai yayi mai cak, dago ido yay ya kalli inda salma take dan yassn aykin tane wannan.
Karaf suka hada ido itama shi take kallo,kwashe wa tai da dariya har tana rike ciki,jamilace da batasan wai nar da ake toyawa ba tace mata lpy ? Lpy yanki kuwa salma? dariya take ba kakkautawa ta nufi daki.
Shikam sameer har idon shi sun fir fito saboda bacin rai yakuma kasa xubar da abin cin.
Jamila ma da bata lura da shi ba tace ” ikon allah sai kallO tafa fara bani tsoro ” dakin tabita tana kwala mata kira.
Tun daga ranar salma ta dau damaran hana sameer cin abin ci da anaje mai da ta bata kodai tasa yaji kokuma tasa gishiri.
sosai abun da take mai yake tabashi dan shi bai iya cin abin cin waje ba,cake kawai yakeci da drinks ya kwanta
duk wai nar da ake tuyawa ba sanin jamila dan bata bari tasani dan batasan surutu,Kwanan jamila biyu ta tattara ta koma kaduna cike da kewar juna .
Tafiyar jamila yakara ba salma damar hukun ta sameer yan da take so.
Xaune take a parlor ta daura kafa daya kan daya ta fara kwalama mai aykin ta kira xuwa can sai gata ta karaso.
Dukawa tai ta ce “hajiya gani “
“Yawwa dama inasan magana da kene “
Tace “ni to gani ay “
“Uhm nabaki hutu kije sai na ne meki kodai kikoma gida kokuma ki xauna anan”
“Hajiya bangane ba tafiya xakuy kokuma ankorenine “
“Kodaya hasalima xaa rinka biyan ki duk wata kamar dai da “
” to nagode sosai hajiya allah ya saka “
“Tace bakomai xa ki iya tafiya “
Cike da doki ta bar gurin tana tasa mata albarka.
Cigaba da kallanta tayi hankalin ta kwance dan yamxu bata da matsalar komai a rayuwar ta,burin ta kawai ta ga ta takura sameer ta hanasa sukuni.
sai da ta lura lkc dawo wan shi yayi,Xuwa can ta mike ta nufi dakin ta sirinji ta dauko da allura da wani farin abu kamar gishiri,fitowa tai ta nufi kitchen sai dariya take a xuciyar ta.
cup ta samu ta tara ruwa rabin shi ta kawo,garin abun nan me kaman gishiri(sweetener) ya kai rabin gwangwani ta juye sai da tatabbatar ya narke sannan ta dauki rin ji taja.
haka tabi ruwan gidan da drinks din gidan tana musu allura,tan gamawa da nan ta nufi dakin sa cikin saa ta tarar a bude yake,nan ma sai da ta bata mai ruwa da drinks sannan ta fito wan ke hannun tq tai tq koma ta xauna.
Tana xama bqdade wa sai gashi yashi go da sallamar sa,aciki ta amsa .
Beko damu ba yawuce ta xuwa dakinsa duk ya kosa ya watsa ruwa yasamu ko fress milk ne ya sha ko yaji saukin yunwan da ke damun sa.
Yana fitowa wa wanka ya xura jallabiyar sa yafito har lkcn tana xaune a inda take.firig ya bude ya dauko hollandiya mai sanyi yabude yakai bakinsa.
Jiyay komai ya tsaya mai,wani xut xut yake ji a saman kansa saboda yanda abun yake kama halce tofar wa yay,yadago ido kamar me shirin kuka yana kallan salma wanda itakuma tanuna kamar bata ganshiba sai makallan ta da take nankuwa hankalin ta na gunshi hamdala kawai take yi.
Kasa motsi yay daga inda yake,yaxama dole ko bai gama abun dayake yi ba ya rabu da salma tun da tafara haka watara xata iya xuba mai guba ya mutu.
Jankafanshi yaya da kyar yanufi,dakinsa harya kai bakin kofa yaji salma ta sheke da dariyar mugunta,bebi ta kanta ba yay gaba abunsa dan inya biye mata yau ba makawa sai yamata mugun duka.
Washe gari koda ya tashi yay mamakin ganin ba ay komai na gidan ba bakuma me aykin,ruwan tea yadafa yasha ya wuce office gaba daya beda walwala a tattare dashi.
Koda salma ta shi indomie ta dafa da kwai taci kafin ta fara sanaar tata watato kallo.
Bata dade da xama ba taji ana kwankwasa kofa tashi tai tabude,megadin su tagani tsaye.
“Hajiya bako kukayi nakuma gaya mishi oga baya nan amma ya ce atemaka a kiramishi ke yana san magadake ne “
“Nikuma “
“Eh hajiya “
Dakamar tacemai bata xuwa sai kuma tace “kace mai inaxuwa kabashi kujera ya xauna “
“To hajiya an gama “
Ciki ta koma tasako katan hijabinta da drinks tafito
gurin daya ke xaune a yar baranda ta nufa kasan cewar ya bata baya yasa bata gane shiba,har ta isa inda yake xaune da sallamar ta.
Amsawa yay,tanemi guri ta xauna,dagowar da xatai indon ta ya sauka a kan j.boy,mikewa tai a raxane tana nunashi “kai,kai dama kaine?mekake nema guna miye hadin ka dani?”
“Kiyi hakuri ki xauna ki sauraReni please,magana naxo muyi dake,karkice aa dan allah ki saurareni”
Komawa tai ta xauna jikinta yay sanyi.
“Dafarko dai naxo nanemi gafarar ki da ta yayanki,duk kuwa danasan shibaxe yafemin ba amma ke ina sa ranki yafemin kuma in allah yasa na samu nasara agunki toshima frnd xai yafemin”
Cikin mamaki tace”kamar ya aykunfi kusa,kuma ni bakamin laifi, komai ba”
“Dane kika sani salma amma yanxu bama tare da yayenki tun bayan faruwan wannan abun …………………………………………yakwashe komai yagaya mata
“Salma ko daya ba laifin yayan ki akan abun da yafaru nini na shirya komai,wanda a sanadiyar haka yayan ki ya tsaneni baya kosan ganina,kuma shiba maxina ci bane kamar yan da kike tunani,kuma baya kisan kai balle har ya kashe jinin sa”
Tun da ya fara bada labari salma ke kuka wiwi,tausayin yayan ta ya cikata.
“Kiyi hakuri nasan ban kyautaba wanda sana diyar hakane ma na dau alkawarin baxan taba hutawa ba har sai naga kun koma kamar da yan da nasan ku tun da nine na bata komai “
cikin muryar kuka tace ” yaya jabir kacuce mu,kacucemu,kuma allah kadai ne xai yimana sakayya kuma baxamu yafe maka ba,kasa ina neman kashe dan uwana da bannuna(ta fada tana nuna hannayenta)kabace min da gani banasan ganin ka “
“Dan allah ki saurareni mana “
Cikin karaji tace” nace katashi kaban guri ko “
Mikewa yay a raxene dan ta bashi tsoro sosai “amma dakin…”
“Wlh xakasa in illata ka a banxa a wofi “
mikewa yay yabar gurin jiki a sanyaye ya hau moter sa ya fice gidan.
Kifewa tai a gurin tay kuka kamar ranta xai fita har taban tausayi.
Ku Cigaba da bibiyanmu domin samun fitattun littafai masu kayatarwa.