Ni Da Kanin Mijina:

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com

Wanann littafin banyi shi dancin zarafin wata ko wani ba

Related Articles

Budurwa ko matar auren da ta karanta idan taji baiyi Mata ba bana bukatar maganar banza bansaki dole ki karanta ba eheeee

Dasunan Allah mai rahama Mai jink’ai

   CHAPTER 11

Saida! Fahat yayiwa mahaifinsa Kira kusan 10miss calls, kana mahaifin nasa ya ɗaga wayar cikin gadara, da nuna isa,

Wani daɗi ne Fahat yaji ya mamaye Masa zuciyarsa duk da abunda mahaifin nasa yayi Masa bai damuba, dama shi burinsa ya ɗaga wayar kawai,

Sallama Fahat yayiwa mahaifinsa kana yace

“Barka da yamma Abbah”
Shuru abbah yayi masa kamar baiji ba

Da yake mu a Nigeria yamma ce Amma su, a can dare ne yanzu,

Kamar ba zai karbi gaisuwarba amma sai ya karba ciki_ciki kamar wanda bakinsa ke ciwo,

har Yanzu Alhaji Ahamad fushi yakeyi da ɗan nasa,

Fahat kuwa har ga Allah bayajin dadin yanda mahaifinsa keyi Masa na nuna ko in kula da yakeyi akansa, ba ruwansa da wane irin hali zai Shiga,

Murmushin bakinciki Fahat yayi amma sai yawani wayancan kamar ba koma a ransa yace

“Abbah mun kammala jarabawar karshe, gaba daya, gobe Insha Allahu zamu dawo, nayi kewarku sosai Abbah inason na ganku, na ƙagu gari bai waye ba”

Shuru Abbah yayi Masa Kamar badashi yake magana ba, jin Shuru yayi yawa ne yasa Fahat ya dauka ko wayar tasa ta mutu ne yakenan yanata zuba surutu kamar parrot, duba wayar yayi yaga Suna kan layi bata katse ba, kana yace

“Hello_hello Abbah ko baka jinane?”,
Sai a lokacin Abbah yayi gyaran murya yace “tom naji Allah ya kawoku lafiya”,

Daga hakan ya katse wayarsa baijirama yaji meh Fahat zaice ba

Wani ƙololon baƙin ciki ne Fahat yaji ya mamaye zuciyar sa,

“Ohhh sheet wai menayiwa Abbah ne haka ? Abbah why? Meyasa kakeyi mani hakan ne? Kamar bakaine ka haifeni ba, meyasa kafison bro hisham akaina Abbah?”, Fahat ne yakeyiwa kansa wayannan tambayoyin da bashida amsarsu,

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara fita daga idanun Fahat, yana tausayin kansa da irin ƙiyayyar da mahaifinsa yake nuna Masa a fili,

Dailing number mahaifiyar sa yayi, bugu ɗaya yayi Mata, ta ɗauka, bai jira tayi magana ba yafara magana cikin Kuka yana cewa

“UMMAH menayiwa Abbah? Meyasa Abbah baya sona? Bai damu da damuwata ba, UMMAH why?”,

UMMAH dake zaune kusa da Abbansu jin kalaman Fahat yasa tayi saurin tashi tsaye tabar parlourn ta haura sama, ɗakinta tashiga ta rufo ƙofar kana tace

“Fahat ka saurareni da Kyau kaji mahaifinka, yana masifar sonka, kuma ya damu da damuwarka, kawai dai Abbanka ya kafe akan abu ɗaya ne akan cewa bazakayi aure a Yanzu ba tun lokacin da mukayi wacan maganar, har yanzu fushi yakeyi, bai sauko ba, dan haka ya gayamun yace Mani gobe zaka dawo, dan haka dan Allah Fahat inason ka nutsu, kada ka taba nunawa mahaifinka cewa kai aure kakeso, kayi hakuri kuma kayita addu’a, kuma nima zanci gaba da tayaka da addu’a insha Allahu”,

Tsagaita kukansa Fahat yayi kana yace “UMMAH Yanzu kina nufin Kenan na hakura da auren Kenan? Wallahi UMMAH da kunsan halin da nake ciki da bazakuce bazanyi aure ba Yanzu”,

sha re hawayen idonsa yayi kana yaci gaba da cewa “shikenan UMMAH badai auren ne a ba a so nayi ba? Tom na Hakura da auren yayi?”,

Har cikin zuciyarta takejin tausayin ɗan nata lokaci daya itama Kukan yazo Mata kana tace masa “ba haka nake nufiba Fahat, dan Allah ka fahimceni duk duniya ba abunda nakeso a Yanzu kamar naga kayi aure ka samu muradin ranka, ni bawai nace bazakayi auren bane, ah_ah, kawai inason ka kwantar da hankalinka ne, mubi komai a hankali insha Allahu komai zaizo Mana da sauki, ina fatar kafahimce ni”,

gyaɗa mata kansan fahat yayi ƙamar tana ganinsa yace “eh UMMAH”,

Har cikin ranta taji dadin yanda Fahat ya sauko kamar ba shiba.

UMMAH bata kashe wayar ba saida taga ta kwantarwa da ɗan nata zuciya tare da bashi magagannu masu ratsa jiki kana sukayi sallama”,

Kwanciya Fahat yayi akan gadonsa, yana tunano irin magannun da mahaifiyarsa tayi Masa, ba ƙaramin daɗi yaji ba da irin nasihar da tayi Masa, wani irin son mahaifiyar tasa ne yaji ya ƙara kamasa, murmushi yayi kana ya kashe wutar ɗakin ya haye gadonsa bacci mai nauyi yayi nasarar daukarsa,

yau oga Hisham a gida aka yini amma duk yininnan da yayi duk a ɗakinsa yayi sa, a kwance, ko abinci a ɗaki Zulaihat tayi ta kawo Masa daga breakfast har na dare saboda Zulaihat da wuri take gama abinchin darenta kafin magrib saidai kawai tayi wanka ta gyara gida,

Kwance hisham yake a ɗakinsa Jannat tana kwance akan jikinsa sai surutu takeyi Masa, tun yana biyeta har ya fara gajiya da surutunta yace mata

“Yawwa bbyan Daddy tashi kije wurin Ammienki ki bata labari Kinji, yau abbie dinki bayajin dadi, zazzabi ke damuna kiyi mani addu’a kinji Babynah”,

Ɓata rai Jannat tayi, ta hade rai kamar bata taba dariya ba, sai kuma ta fashe da kuka, saurin sakata jikinsa yayi kana yace “subuhanallah Babyn Daddy waya taɓa mani ke??

Cikin Kuka Jannat tace “bakaine kace bakada lafiya ba, ni banason kayi ciwo Saboda banason ka mutu, ranar wata ƴar ajinmu a makaranta akace Abbanta bashida lafiya, sai take gayamun Abbanta zazzabi yakeyi shikenan akace ya mutu”,

Ƙara fashewa da Kuka Jannat tayi tana Kara shigewa jikin Abbanta, tana cewa, Dan Allah Abbie kada ka mutu wallahi zanyi Kuka idan ka mutu, nida Ammie zamuyi Kuka sosai,

Saura kiris dariya ta kubucewa Hisham har ga Allah ba karamar dariya Jannat ta bashi ba, wai ita nan har tasan mutuwa,

Murmushi yayi kana yafara bubuga bayanta yana cewa “yishurunki Babyn Daddy, insha Allahu Daddynki bazai mutu yanzu ba”, saurin ɗago da rinannun idanunta Jannat tayi tace

“Abbie da gaske bazaka mutu yanzu ba?”,

“Ehh insha Allahu Jannat bazan mutu yanzu ba Abbanki yananan tare dake kinji” wani daɗi Jannat taji da mahaifinta yace mata bazai mutu yanzu ba, saurin sauka tayi daga jikinsa, ta sauka daga kan gadon da gudu tana faɗin,

“Yeeeeee thank God naji daɗi da Abbiena bazai mutu yanzu ba” haka tayi ta faɗa har tabar ɗakin da gudu, ɗakin mahaifiyarta taje, tana gaya Mata shirmenta,

Murmushi Zulaihat tayi tace “iyeee diyar daddynta touu shikenan kiyita yiwa Abbie dinki addu’a kinji” inji cewar Zulaihat, Jannat tace tom.

Zulaihat tana gama shiryawa cikin wata mahaukaciyar rigar baccinta mai daukar hankali, kwantar da Jannat tayi tashiga jijigata kamar jaririya, saida taga bacci mai nauyi ya dauketa kana ta kashe Mata wutar ɗakin tare da yimata addu’a, ta fita daga ɗakin,..

Darect ɗakin Hisham tawuce a kwance ta samesa a kan gado sai tunani yakeyi baisan da mutun ba, sai jinta yayi jikinsa ta hade bakinsu guri daya tafar kissing lip’s dinsa, wani kamshi ne yaji ya daki dodon hancinsa saurin bude idanunsa yayi ahankali har ya budesu dar a kanta, murmushi Zulaihat ta sakar masa, shikuwa Hisham ya kawar da kansa gefe,

Wani irin bugawa zuciyarta tayi lokaci d’aya wanda ta rasa dalilinsa

Fara magana tayi a zuciyarta tana cewa, Kar dai ace Hisham dama ba chanzawa yayi ba?, Kar dai ace yadawo mani mutunin arziki ne saboda kawai ya samu abunda yakeso? Tabbas idan hakane kuwa Hisham yaci amanata,

tana cikin wannan tunanin ne taji yafara tureta daga jikinsa har ya tureta gaba daya, tashi yayi ya koma kan kujerar dake ɗakin ya kwanta yabarta a kan gado,

mikewa Zulaihat tayi tafara tafiya har ta isa garesa, tace

“Lafiya my D?? Meyake damunka? Ko baka da lafiya ne?”, Duk a lokaci daya Zulaihat ta jerowa da Hisham wayannan tambayoyin,

Ko kallon gefenta Hisham baiyi ba balai ya samu damar yimata magana sai da ta gaji da tsayuwarta dan kanta tabar Masa ɗakinsa, ta koma nata,tana Shiga ta fad’a kan gado ta rungume yarta bacci mai dadi yayi awon gaba da ita,

Tunda Fahat sukazo airport sai Kiran Yan uwa da abokanan arziki yakeyi yana sanar masu gasu airport zasu dawo nigeria, ba ƙaramin murna abokanan Fahat sukayi ba, saboda sunyi missing din abokinsu sosai,

Tunda suka taso Fahat ya kashe wayarsa saboda k’a’idane idan ka Shiga jirgi dole ka kashe wayarka, tunda jirginsu ya lula sararin samaniya Fahat yayi Shuru, ya daina surutu, sai addu’a kawai yakeyi, bawai dan yanajin tsoro ba, a a kawai dai hakan ya zamewa Fahat jiki,

Faisal kuwa idan ba surutu ba, babu abunda yakeyiwa Fahat, yana bashi labarin jiya da ya koma gida yanda suka kwashe da Arishat,

Yininsu daya cirr a sararin samaniya kana suka iso gida nigeria.

Ku biyomu domin samun fitattun littafai masu kayatarwa.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button