An Bude Shafin Cike Tallafin Na Shirin Green Youth Upskilling Program (GYUP)

Menene Shirin GYUP?
Shirin GYUP wani shiri ne na musamman da Oando Foundation tare da haɗin gwiwar NCIC suka ƙirƙira, domin taimaka wa matasa ‘yan Najeriya samun horo da dama a fannin tattalin arzikin kore (green economy). Yayin da duniya ke fama da matsalolin sauyin yanayi, wannan shirin yana nufin bai wa matasa ƙwarewar zamani da ake buƙata domin tallafa wa ci gaban muhalli, ƙirƙire-ƙirƙire, da samun hanyoyin samun kuɗi.
GYUP zai mai da hankali kan:
Horas da matasa kan ƙwarewa masu amfani,
Ba da tallafi don fara kananan sana’o’i ko kasuwanci,
Samar da damar aikin yi a fannin tattalin arzikin kore.
Waye Zai Iya Shiga?
Ana buƙatar matasa waɗanda suka cika waɗannan sharuɗɗa:
‘Dan Najeriya ko ‘yar Najeriya ne.
Shekaru tsakanin 20 zuwa 35.
Sun kammala aƙalla makarantar sakandare (SSCE).
Suna da ƙwarin gwiwa da sha’awa sosai a fannin tattalin arzikin kore.
A shirye suke su halarci dukkan horon — ko ta yanar gizo ne ko ta zaman ido-da-ido.
Kuma a shirye suke su mika dukkan takardun da ake buƙata akan lokaci.
Abubuwan Da Ake Bukata Lokacin Nerman Shiga:
1. Bayanan Kai:
Cikakken suna:
Ranar haihuwa:
Shekaru:
Jinsi:
Asalin jihar da ƙaramar hukumar haihuwa:
Lambar waya:
Imel (Email):
Matakin karatu mafi kusa:
Yaushe ka/ki kammala makaranta:
A ina ka/ki kammala makarantar?
2. Takaitaccen CV (1 shafi):
– Ya ƙunshi bayanai kamar:
Bayanin kai (Full Name, Contact Info)
Ilimi (Education)
Ƙwarewa ko ƙananan sana’o’i da ka/ki taɓa yi
Harsunan da kake/kike iya yi
Ƙwarewar da ta shafi kwamfuta ko fasaha (idan akwai)
3. Gajeren Bayani Kan Kai (Bio):
– A takaitaccen shafi guda, bayyana wanene kai/ke, menene burinka, da abinda kake/kike yi a yanzu.
– A guji bayani mai tsawo ko sake maimaitawa.
4. Jawabin Sha’awa (Bai wuce kalmomi 300 ba):
– A wannan gajeren jawabi, ka/ki bayyana:
Me yasa kake/kike sha’awar shiga shirin GYUP?
Ta yaya ka/ki ke ganin wannan horon zai taimake ka/ki?
Menene burinka a fannin tattalin arzikin kore?
Ta yaya zaka/ki yi amfani da ilimin da ka/ki samu don amfanar da kai/ki da al’umma?
Domin cikawa danna link dinnan
Danna nan don cikawa👉 https://gyup.net/apply/