Littafin Khalysaah Kashi Na Arba’in Da Bakwai (47)

Assalamu alaikum warahmatullah, jama’a barkanmu da warhaka, sannunmu da sake saduwa daku a cikin wani sabon shirin namu da yake zuwar muku ta wannan shafin namu mai albarka na arewamusix.com

Washegari da safe har karfe goma saura Khaleesat bata tashi baccin da take ba, daga Umma har Aunty Farida babu wanda ya tasheta don duk sun san bata yi wani baccin kirki ba daren jiya, daga wayewar gari zuwa lokacin mutanen da suka shigo dakin Umma yi mata Allah ya kyauta da abinda ya faru sun fi goma, don gaba daya labarin ya gama bazuwa garin, Aunty Farida ta kalli Umma bayan wata makociyarsu da ta shigo jajen ita ma ta fita, a fusace tace “Don Allah ki dena tanka masu Umma, ki nuna ke baki ma san jajen uban me suka shigo yi maki ba, wallahi banda ke in ban ci kaza kazan mace ba ta sake shigo mana dakin nan ace ba ni ba, wannan ai iskanci ne” Umma tace “To ya kike son inyi Farida? kinga ai muna mutunci sosai da su shine har ya sa suke shigowa, duk warce kika ga ta shigo dakin nan to muna mutunci sosai ne da ita, kin ga ai bazan masu rashin mutunci ko wani abu ba, wanda ya yaÉ—a labarin a garin ai shine vabvan munafuki ba wanda ya shigo jajenta maka ba, kuma naga dai ba kan Khaleesat farau ba mutuwar aure” Aunty Farida ta mike tace “Ban taÉ“a ganin inda ake shigo ma mutum jajen mutuwar aure ba sai a garin nan, kuma wannan ba komai bane banda salon gulma da munafurci” Daga haka ta fice daga dakin zata duba ruwan zafin da ta dora kan wuta, Umma ta kalli Khaleesat da tayi backing dinsu tana bacci, ta kai hannu ta dafata, tayi kasa da murya tace “Har yanxu baccin dai Khaleesat?” Juyowa Khaleesat tayi tana murza ido, sai kuma ta mike zaune, Umma na kallonta tace “Jiya da daddare baki ci abun kirki ba, ki je ki wanke baki ki zo ki karya, ga wainar shinkafa na sa an amso maki tun daxu, kar ya huce” Khaleesat ta jawo hijab dinta ta saka sannan ta sauka daga kan gadon, ta tafi gun akwatinta da ta dawo da shi daga America ta duÆ™a ta bude jakar ta ciro Shower gel dinta da sponge, sai toothpaste da Brush, Umma dai kallonta kawai take har ta mike zata fita daga dakin Umma tace “Tunda wanka za kiyi kice Farida ta juye maki ruwan zafin, tana waje” Khaleesat tace “To Umma” Daga haka ta fita daga dakin Umma ta bi ta da ido, Khaleesat bata ko kalli inda kishiyoyin Ummanta suke ba da dukun dukun din zannuwan jikinsu kamar masu yin kuli kuli, ta jira Aunty Farida ta juye mata ruwan zafi a bucket ta surka mata sannan ta kai mata har bandaki, bayan ta shiga wankan Aunty Farida ta dora wani ruwan ta koma dakin Umma, Mama Zubaida ta taÉ“e baki tana murmushi ta kalli Mama Shatu tace “To kuma yanxu ko da uban me za ayi mana takama?” Mama Shatu ta kwashe da dariya tace “In kin tambayeni in tambayi wa? Ba ke kike kokwanton maganar Malam ba da yace auren karkari ayi wata daya ya sakota, to kin dai ga kwalliya ta biya kudin sabulu, sai ki dena cewa kinyi asaran kudin ki, ji yanda hankalinki ya tashi ranan da muka je gidan da Nenne kin ga katon gida ta shiga dakin can ta fito ta shiga wancan ta fito kin zata watayawa take a gidan, ni dama ina kallon kwayar idonta nasan ubanta take ci a gidan, sam ban ga alamar kwanciyar hankali ba don duk a firgice na ganta” Mama Shatu ta sauke ajiyar zuciya ta rike haÉ“a tace “Ohhh…. Ba karatu a Amurka, ba Miji, ga zawarci, wannan asara da yawa take ni Aisha, wannan shi ne ga koshi ga kwanan yunwa, an ga samu an ga rashi, ina Zahra’u zata saka ranta ta ji dadi” Mama Zubaida tace “Ke baki ga haka ya korota daga ita sai kayan jikinta ba, ko er jakar hannu da ake saka waya fa bata taho da shi ba, dama a haka ya dauketa, kuma kinga ko tsinke ba a kai mata ba dama” Duk suke kwashe da dariya har da kyakyatawa, Mama Shatu tace “Sai a dawo a ci gaba da alalan da aka watsar, don ita kanta Faridan Allah ya sa É—an zaman da ta dawo suka yi ba a cinye jarin nata ba, nan nan a gabanmu aka yi ta hade haden garin É—anwake da su kuka da kubewa za a kai ma Khaleesat ashe ashe korota zai yi, ni anjima ma zan shiga a tsam min garin danwaken don naga da yawa suka yi” Tana dariya ta kare maganar, Mama Zubaida tace “Ae wallahi ko tsirara zan yi na gwammace inyi da dai Zahra’u taji dadi da ‘ya yanta, in ke kin manta irin cin Æ™ashin da Malam ya dinga mana bayan ya aurota ni ban manta ba, duk muka zama bora a gidan nan, baya ganin kowa sai Zahra’u tunda da asirinsu na buzaye ta shigo gidan, banda dai dama tun asali idonmu ya bude da Malamai ai da tuni ya sake mu tun bai samu karayar arziki ba, hatta kayan dakin da ya siya mata sai da na zaga na koma kasuwa na tambaya aka ce min nata duk yafi namu tsada, gashi yaranta su ne ‘ya yan so barin Khaleesat din nan ai mun sha bakin ciki iri iri Shatu, Ita fa har Umra tayi sannan ga Hajji, mu kuwa iya Hajji kawai muka je mu ka yi tsabar ya maida mu ‘yan iska” Mama Shatu ta sauke wani ajiyar zuciya tace “Ki bar tuna min wannan takaicin Zubaida, banda a tsaye muke ai da wani labarin ake yanxu ba wannan ba, haka mu ma muka yi ta hadata da Malam da taimakon asiri, amma shegiyar bata yi zuciya ta koma kasar su ba da ya fara cin ubanta a gidan, in sha Allahu yanxu ta fara ganin bala’i ita da zuri’arta su da jin dadi ko farin ciki har abada, hatta yan biyun nan ya kamata mu fara miÆ™a sunansu yanxu kar lokaci ya kure, don naga wani farin jinin jama’a da suke da shi, duk inda suka shiga sai an tankasu ayi ta nan nan da su” Shigowar Nenne gidan yasa suka yi shiru, duk suka gaisheta ta amsa ba tare da ta kallesu ba ta nufi dakin Umma da er ledanta a hannu, duk suka taÉ“e baki suna bin ta da kallo har ta shiga dakin, Umma da Aunty Farida suka gaida Nenne bayan ta shigo dakin, Nenne ta amsa bayan ta ajiye ledan hannunta tace “Ina Khaleesar take?” Aunty Farida tace “Ta shiga wanka” Nenne tace “Atoh dai, dama ina zata tsaya bakin cikin shege ya kasheta, harkar gabanta kawai zata ci gaba da yi kamar babu abinda ya faru, da auren wannan gansamemen mutumin da rashin aurensa ai duk daya, kuma mu muka cusa mata shi ba sonsa take ba wallahi, yanxu banda ni da ku waye yasan tayi wani gantalallen aure ko da wani ya fito yana son ta, banda dai gulma tayi ma jama’ar Mariri katutu, ai kawai ce ma Ali zan yi ya siyar da gidan nan da nawa gidan mu koma ko Rijiyar Lemo ne” Dukawa tayi ta kwance ledan da ta ajiye tace “Gashi nan, kasuwa na aiki almajirina ya siyo min kayan ciki me kyau nayi mata farfesu ta sha ta mance abinda ya dameta, saki ai ba kanta farau ba, mu ma duk ai an taÉ“a sakin mu, uban Ali saki nawa ne bai min ba, sai da igiya daya ya rage mana sannan muka nutsu muka zauna har mutuwa ta raba” Wata mata ce tayi sallama bakin kofar dakin Umma, Umma ta amsa mata, matar ta shigo tana gyara yakunannen gyalenta, ganin Nenne ta duka har kasa ta gaisheta, Nenne ta amsa tana rufe farfesun da ta kawo ma Khaleesat kar matar ta barbade farfesun da gyalenta, Bayan matar sun gaisa da Umma tace “Ashe abinda ya faru kenan Ummansu Khaleesah?” Nenne ta juya ta kalleta tace “Me ya faru?” Matar ta langwabar da kai cikin rashin jin dadi tace “Mutuwan auren Khaleesah Nenne” Nenne ta mike tsaye tace “Innalillahi wa inna ilaihi raji’una, mutuwar auren wace Khaleesar? A ina kika ji auren Khaleesah ya mutu? Na shiga uku na lalace, wato matan Mariri baza ku canza halin ku na tsugudidi ba ko? To daga ke har wanda ya gaya maki kun ci kaza kazan ku yan iska kawai shegu, tashi ki fita ki ba mu waje, sai dai ki ga mutuwar aure a dakin ki ko na uwar ki, kaji min mata dai munafuka, uban mutuwan auren Khaleesah, fita ki bamu waje” Da sauri matar ta fita daga dakin ta saka takalmi wari da wari ta bar bakin kofar, Nenne na huci ta kalli Umma tace “Ke kuma Las spika ki ka dauka kike shelan an saki Khaleesah?” Aunty Farida ta tabe baki tace “Ina fa Nenne, mu ma kawai gani muka yi ana ta shigo mana tun da gari ya waye, wai an zo Jaje, wa enda suka fitar da labarin ai su ne babban munafukai” Nenne na share zufan goshinta tace “Shatu da Zubaida kenan, babu me fitar da zancen nan sai su” Tana kai wa nan ta fice daga dakin, kafin ta fito dama su Mama Shatu duk sun shige dakunan su da sauri bayan sun ji abinda Nenne tayi ma matar da ta fita daga gidan, nan tsakar gida Nenne ta tsaya babu abinda ta manta bata gaya masu ba, zagi kam sun sha har sun gode Allah, Allah ya isa shima tayi masu kwando kwando, daga karshe tace “Kuma in har Ali ya dawo gidan nan anjima bai dau matakin fitar masa da sirrin gida da ku ka yi ba wallahi sai dai ya zaba ko ni ko ku, da dai in zauna da surkai magulmata munafukai gwara in sallame ma duniya Ali in shi bazai sallama maku ba, to ai ita Khaleesar ta samu mashinshini har tayi auren ta fito, ku kuma da naku ‘ya yan ke zube kaman gwanjo babu mataya fa? Dama nace ma Ali in har bazai bada su sadaka ba to ni a dena nuna su ace jikokina don kunya nake ji, ko kuma in tattara in bar masa Maririn in har bazai samar ma narka narkan ‘ya yanku mafita ba, yanxu in na Jera da Labeebah ba sai ace ita ta haifeni ba, sannan kwata kwata basa wuni a gidan nan ban san inda suke zuwa ba, sai mutum ya shigo sau dari bai gan su sau biyu ba” Khaleesat ta fito daga bandaki tana rike da Shower gel dinta ta nufi dakin Umma, Nenne ta bi ta a baya tana cewa “Kin fito Khaleesah, mu je ga farfesu can na maki” Sai da suka shiga dakin sannan Khaleesat ta gaida Nenne, Nenne ta amsa tace “Kar fa ki ce zaki sa damuwar shegen a ranki kin ji? Allah ne ya dubemu ya rabu dake cikin aminci bai maki wata illa ba, dama kuma ance min uwarsa har tsafi take yi, kinga hada zuri’a da irin wannan mutane ai abun tsoro ne, kar ki saka komai a ranki, rabuwan shi ne mafi alkhairi a gare ki dama an gaya min” Khaleesat dai ta zauna gefen gadon Umma tana shafa cream dinta, Nenne na kallon Umma tace “Ke kuma duk wanda ya shigo maki jaje baki koresa ba Allah ya isa kema, ai mutum daya na shigowa kika rufe ido kika koresa komawa zai yi ya sanar ma sauran, shikenan babu wanda zai sake shigo maki, ni kin ga tafiyata inje in nemi abinda zan ci da rana” Daga haka ta fice daga dakin. Bayan Azahar Khaleesat na zaune kan darduma da qur’ani a gabanta tana karantawa a zuci, sai ga Safiyyah ta shigo dakin Umma da sallama, Khaleesat ta rufe Al-qur’anin ta daga kai tana kallonta tana murmushi, ji tayi kamar all her worries are gone ganin Safiyyah, Safiyyah ta ajiye handbag dinta ta zauna edge din katifar dakin tana kallon Khaleesat a sanyaye, gaba daya ta kasa ce mata komai, Khaleesat ta mayar da Al-qur’anin Aunty Farida gefe sannan ta mike ta koma kusa da Safiyyah ta zauna tana kallonta har sannan murmushin fuskarta bai É“ace ba tace “I miss you so much” Hawaye ne ya zubo ma Safiyyah a ido don kawai ta kasa daure hakan, Khaleesat ta sauke idonta kasa, sai ga hawayen ita ma a idonta, rabonta da zubda hawaye tun jiya a gaban Abbanta, bayan kuma ta shigo ta kwanta bata sake yarda tayi kuka ba duk da kusan yanda taga rana haka taga daren ga zafin da zuciyarta ya dinga mata, Safiyyah ta rungumeta tace “It’s fine Khaleesat, Allah ya saka maki abinda yayi maki” Khaleesat ta gyada mata kai kawai, Safiyyah ta goge idonta don taga alamar kukan da take ne yasa Khaleesat kuka, Safiyyah ta dago kanta tana kallonta tace “Su Umma fa?” Khaleesat tace “Sun je gaisuwa ne anyi rasuwa dazu a unguwan” Safiyyah tace “Allah sarki, Allah ya ji Æ™an musulmi” Khaleesat tace “Ameen, ya su Mama fa?” Safiyyah tace “Duk suna lafiya lau, tace in gaisheki, bayan mun gama waya daxu tace in kira mata ke, na sake kiran wayar Aunty Farida naji a kashe” Khaleesat tace “Ehh babu caji ne, ta bada a kai mata wajen caji” Safiyyah tayi shiru, bata son yi ma Khaleesat maganar da zai kara sa taji ciwo a ranta, amma duk da haka calmly tace “Saki nawa yayi maki?” Khaleesat ta buda manyan idanuwanta tace “Kawai ce min yayi ya sakeni” Safiyyah taji bakin cikin ba saki uku yayi mata ba, don ita ba kukan bakin cikin sakin da yayi take ba, a’a bakin cikin mayar mata kawa bazawara da yayi ne babban bakin ciki da takaicinta shi ne yasa har ta zubda hawaye, a gida ma kukan da tayi kenan don taji ciwon abun sosai, Khaleesat ta kalli inda Aunty Farida ta ajiye Envelope din da Drivern gidan su Abdul ya kawo tace “Ga ma can takardan ya aiko” Safiyyah ta juya ta kalli Envelope din, mikewa tayi ta dauko ta dawo ta zauna ta ciro takardan ciki, ita dai Khaleesat kallonta kawai take don har sannan bata duba abinda ke jikin takardan ba, daga Aunty Farida har Umma babu wanda yace mata saki uku ne, jiya kuma da Nenne ke ta hayaniya a tsakar gida bayan an kawo takardan Khaleesat na kwance duk bata san abinda ake ba don abubuwan da suka dameta daban, Safiyyah ta kalli Khaleesat da sauri tace “Saki uku ne ai a takardan” Khaleesat ta amshi takardan a hankali tana dubawa, after some seconds ta kalli Safiyyah tace “Wannan ai ba rubutun sa bane” Safiyyah ta hade rai tace “Do we care?? Ba dai shi aka kawo mana ba, kinga ai da shi za mu yi aiki, don da kika ce saki daya ne sai da gabana yayi mummunan faduwa don matsiyacin zai iya dawowa yace ya maida ke mu shiga uku, amma tunda ga takarda an rubuta saki uku a jiki shikenan an wuce wajen, Alhamdulillah” Khaleesat dai kallon Safiyyah kawai take, Safiyyah ta ajiye takardan ita ma tana kallonta, can a hankali Safiyyah tace “I don’t understand you Khaleesat, ko dai bakin ciki da sakin da Abdul yayi maki ki ke? Kin yi give up kan cewa zaki zauna zaman har abada da shi ne? Pls let me know first so that i will watch my words” Khaleesat tayi murmushin takaici tace “Dukan yau daban, na gobe daban, zagi, hantara cin mutunci, living with hunger….” Kasa ci gaba Khaleesat tayi ta fashe da matsanancin kuka tana girgiza kai, Safiyyah ta rungumeta tace “Allah ya saka maki, Allah ya saka maki cikin gaggawa, in sha Allahu sai yaga karshensa tun ba aje da nisa ba, in sha Allah sai hakkin ki yayi tormenting dinsa har karshen rayuwarsa, komin lalacewan gidanku baza a doke ki ba balle a zage ki ko a hantare ki, uwa uba a bar ki da yunwa, In anyi duniya don manzon Allah sai Allah ya nuna ma Abdul iyakansa, wato punching bag ya mayar dake a gidan, kalli yanda kika rame kalanki ya disashe kamar ba ke ba, dubi yanda duk kika fita hayyacin ki, wallahi hakkin ki bazai taÉ“a barin Abdul ba, ki kwantar da hankalinki ki cire ko wani damuwa a ranki ki dau hakan a kaddarar rayuwarki” Kai kawai Khaleesat ke gyada mata hawaye masu zafi na zuba idonta, Sosai Safiyyah ta dinga bata words of encouragement tana kwantar mata da hankali, har Khaleesat taji sanyi sosai a ranta, taji ta samu relieve din abubuwan da suka tunkushe mata a rai tun jiya, a haka Umma da Aunty Farida suka dawo suka samesu, Umma ta ajiye masu É—anwaken da ta siyo a makota sanin Khaleesat na son É—anwake, ba laifi Khaleesat ta ci É—anwaken me yawa tare da Safiyyah, dama duk yau ta kasa cin komai, ko farfesun da Nenne ta kawo mata kaÉ—an ta iya ci, amma sai ga shi ta ci É—anwaken sosai, sai kusan karfe shidda na yamma Safiyyah ta bar gidan, with the relieve that tayi consoling kawarta tunda gashi har tana dariya ta baro ta, sallan magrib kawai Safiyyah tayi ta jawo wayarta tayi dialing number Housemate, wanda rabon su yi magana tun sanda ya gaya mata abinda Khaleesat tayi masu shi da Ajay.

Related Articles

Don Allah kuyi share wa sauran friends dinku.

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Check Also
Close
Back to top button