Yadda Zaka Nemi Aikin Sojan Sama Waton Nigerian Airforce
Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Rundunar sojojin saman nigeria wato Nigerian Airforce sun bude shafin su domin sake daukan sabin ma’aikata Na Shekarar 2024, Rundunar ta bude shafin ne tun a 30/10/2023 sannan za a rufe 11/12/2023
Ga wanda yake bukatar neman aikin ga abubuwan da ake da bukata:
- Dole ya kasance dan Nigeria
- Dole ya kasance kana da Katin dan kasa wati NIN
- Dole ya kasance baka da wata larura ko wani lefi
- Dole ya kasance kana da katin haihuwa
- Dole ya kasance kana da Indigine
- Dole tsayi kar yayi kasa sa 1.68maza mata 1.65
- Dole ya kasance kana da Credit 4 A Waec ko Neco ko Nabteb
Yanda zaka Nemi aikin
Da farko zaka shiga Wannan link din dake kasa
👇
Apply Now
Bayan Link din ya bude zai kawo maka wani Rubutu Disclaimer saika danna Ok
Daga nan zai nuna maka wani hoto wanda aka Rubuta Airmen/Airwomen saika danna wajen
Daga nan zai kawo maka wani hoton saika danna Start Application
Daga nan zai kawo maka rubutu mai yawa saikayi kasa ka shiga Start Application
Bayan ya bude zai kawo maka wani waje sai kayi Tick sannan kayi Continue
Daga nan zai baka wajen da zakasa number wayar ka sai kasa sannan ka danna Next
Daga nan zai baka wajen sanya email shima sai kasa kayi Next
Daga nan zai kawoka wajen da zaka kirkiri password saika kirkira, amma ka rubutua suna da kuma lamba, misali Arewamusix1234 bayan ka kirkira sai kayi Next
Daga nan shikkenan zaiyi login daga zuwa cikin portal din domin ka cike dukkan bayananka.
Bayan ka kammala cikawa zasu baka Slip sai kayi Print out dinsa domin dashi zakaje Screening