Yadda Ake Gane Anyi Hacking Na Whatsapp Account

Naga sakonni da dama mutane suna tambaya cewar:

  1. Shin ana hacking din whatsapp account?
  2. Ya zanyi na gane anyi hacking whatsapp account din abokina/ƙawata?
  3. Idan anyi mene dalilin yin hacking din?
  4. Wacce hanya za’abi domin kare kai?

Da sauransu

To gaskiya ana hacking din account din mutane wanda sukayi sakaci da account din bawai iya Whatsapp ba kawai, harda sauran platforms da ake amfani dasu musamman facebook da whatsapp domin sune yawancin mutane suke amfani dasu…

A takaice dai anayi hacking din whatsapp account.

Yadda zaka gane cewar hacking whatsapp account shine: a duk lokacin da kaga ” Your security code with wane-wane changed tap to learn more” da yellow din kala…

Dalilai guda 2 zuwa ukune suke sawa a nunama wannan abun
✅ Na farko kodai abokinka ya canza waya
✅ Na biyu ko kuma andora account din nashi a wata wayar daba tashi ba.
✅ Ko kuma ya canza number waya da yake amfani da ita.

Dalilin kuwa dasaya ake hacking din account din bazai shige DAMFARA ba, domin kuwa indai kaga wancan alamar dake cikin hotonan sannan kaga an tambaye ka wani abu to kira number din katambaya tukunna kafin kabada kudin ko kuma abun da aka tambaya.

Sannan ana iyayin hacking din account naka domin a cutar dakai sannan a ɓatama suna, ko aci mutuncin wani wanda yake da mutunci agareka, akwai dalilai masu yawa…

Ga wasu daga cikin hanyoyin da zakabi domin kare kanka daga masu hacking din whatsapp account itace:
YARDA kaga yarda da mutum 100% shine babban abinda dakesamu acikin wahala da takaici, to kada ka yarda da kowa 100%…

Bude Security notifications – wato duk lokacin da wata matsala tasamu security na devices da kake amfani ita asanar dakai.

Kunna Two- step authentication a Whatsapp Account naka – numbobine guda shida (6) kacal zakasa a matsayin tsaro kamar na waya.

Kada rubutun yayi yawa bari na tsaya haka, Allah dai ya karemu ya tabbatar mana da alkhaira

  • Sulaiman.B TechSulaiman BaffaSulaiman Baffa

Join Our Whatsapp Group

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button