Gidan Jaridar LEADERSHIP HAUSA Suna Neman Ma’aikatan Online/Social Media
Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokaci da fatan kowa yana cikin koshin lafiya.
Gidan jaridar Leadership hausa zasu dauki ma’aikatan wanda zasuyi musu aiki a online aikin Social media
Abubuwan da ake bukata wajen neman aikin:
- Ana bukatar kwarewar iya amfani da shafukan sada zumunta
- Kwarewa wajen iya farautar labarai masu inganci a shafukan sada zumunta
- Iya amfani da kayayyakin gyaran hoto, video, sauti da kuma dorasu a shafin sada zumunta
- Sanin sharruda da ka’idojin rubutu
- Fahintar dokokin amfani da shafukan sada zumunta
- Kwarewa wajen bibiyar al’amuran dake wakana a shafukan sada zumunta
- Wallafa labarai a shafukan sada zumunta dede da lokutan abokan huldarmu
Yadda Zaku nemi aikin:
Domin neman wannan aikin aika da CV dinka zuwa daya daga cikin Email din dake kasa
- hausa.leadership.ng
- leadershipayau@gmail.com
Lokacin rufewa: 27, August, 2023
Allah ya bada sa’a